Yanzu-yanzu: Gwamnan El-Rufa'i ya haramta zanga-zanga da sunan addini a jihar Kaduna
- Biyo bayan dokar ta bacin da aka sa a Sokoto, Gwamna El-Rufa'i ya kafa dokar haramta zanga-zanga
- Zanga-zanga ta rikide a Sokoto Sokoto yau Asabar idan matasa suka fara kone-kone da fashe-fashe
- Matasa na zanga-zangar kira ga gwamnati ta saki matasan da suka kashe yarinyar da tayi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW)
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Asabar ta sanar da haramta duk wani zanga-zanga da sunan addini a fadin jihar.
Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa an yanke hakan ne bayan zaman shawara da hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa duk wanda ya saba wannan doka zai fuskanci fushin hukuma.
Ya kara da cewa haramta zanga-zangan ya zamto dole bisa abinda ke faru a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Gwamna Nasir El-Rufa'i ya bada umurnin wa jami'an tsaro su tabbatar da an bi wannan doka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto
Wasu matasa masu zanga-zanga a ranar Asabar, 14 ga watan Mayu, sun kona tare da lalata wasu coci biyu karkashin jagorancin Bishop din darikar Katolika na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah.
Rabaran Christopher Omotosho, daraktan hulda da jama’a na cocin Katolika na Sokoto ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Omotosho ya bayyana cewa fusatattun matasan sun kona kofar daya daga cikin gine-ginen cocin tare da kona wata mota bas a harabarsa. Ya kara da cewa sun kuma lalata coci na biyu da lamarin ya shafa.
Asali: Legit.ng