Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Ya yi tsokaci kan lamarin da ya faru a jihar Sokoto ranar Alhamis.

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW)

1. Mun jima muna jan hankalin mahukunta Najeriya a kan a riƙa gaggauta hukunta masu miyagun laifuka a cikin al’umma, amma hakan ya kasa samuwa.

2. Mutane sun fara gajiya da sakacin hukumomi game da hukunta masu laifi, har sun fara ba wa kansu lasisin ɗaukar doka a hannunsu, wanda ba haka aka so ba.

3. Lokaci ya yi ga waɗanda ba Musulmi ba a ko’ina a duniya, su farka su fahimci girman Annabin rahma a zukatan Musulmi. Duk wani Musulmi abin alfahari ne a gare shi ya sadaukar da komai nasa, har ma da rayuwarsa wajen kare martabar Annabin rahma. Don haka su guji aikata duk wani abu da zai shafi mutuncinsa (SAW) da darajarsa, domin duk sanda wani ya yi haka, to sakamakon ba zai zo da sauƙi ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

4. Ya wajaba Mahukunta su sani cewa, babu wata huduba ko wani jawabi na wani mutum, ko wane ne shi, da zai iya dakatar da al’umma yayin da suka fusata sakamakon cin mutunci Annabin rahma a fili karara ba tare da doka tana aiki ba.

5. Ya kamata su sani cewa, waɗanda ake zargi da kisan wadda ta zagi Manzon Allah (SAW) a jahar Sokoto da gabatar da su ga shari’a, ba shi ne zai dakatar da faruwar hakan ba a nan gaba, sai ma dai ya ƙara zuzuta wutarsa, ya daɗa tunzura al’umma. Babban abin da ya dace shi ne, hukuma ta fito ta yi jan kunnu dda kakkasan harshe a kan duk wani da zai yi tunanin batanci ga wani daga cikin annabawan Allah, da kuma daukar mataki mai tsananani a kansa.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

6. Duk wani Musulmi da wannan cin zarafin da aka yi wa Annabi (SAW) bai baƙanta masa ba, ya fito ya yi Allah-wadai da shi, sai dai yin Allah-wadai da abin da ya biyo bayan ɓatancin kaɗai, to lalle wannan mutum ya tuhumi zuciyarsa game da irin son da yake yi wa Annbin rahma da addininsa.

7. Muna kira ga sauran al’ummar Musulmi da su kwantar da hankalinsu, su guji shiga cikin duk wata fitina da za ta haifar da tashe-tashen hankali da tarzoma. Su sani cewa, kullum duk wani mai gaskiya, to yardar Allah tana tare da shi, kuma ba zai taba tozarta ba ko da kuwa sama da ƙasa za su haɗu a kansa.

8. Allah ya ba wa kasarmu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng