Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m

Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m

  • Jami’an Hukumar Yaki da Rashawa da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC ta kama mai makarantar koyar da damfarar yanar gizo da dalibansa 16
  • Lamarin ya auku ne ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu a Lokogoma da ke birnin Tarayya, Abuja kuma an samu bayani akan yadda ya ke biyan hayar gidan da ya ke koyarwar a N3m duk shekara
  • An samu nasarar kama su ne bayan samun bayanan sirri, kuma jami’an sun kwace tsadaddun motocin hawa guda biyu, wayoyi, na’aurori masu kwakwalwa da sauransu

Abuja - A ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, Jami’an Hukumar Yaki da Rashawa da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC sun kama wani mai makarantar koyar da damfarar yanar gizo da dalibansa guda 16.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m
An Kama Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 a Gidan N3m. Hoto: EFCC.
Asali: Twitter

Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m
Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Abuja. Hoto: EFCC.
Asali: Twitter

An kama mutumin mai suna Afolabi Samad tare da dalibansa 16 na makarantar da ke Peace Estate anguwar Lokogoma cikin Abuja kuma ya kama hayar wurin ne a Naira miliyan 3 duk shekara kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Twitter.

Da safiyar Alhamis jami’an ofishin hukumar ta Abuja su ka kama shi bayan samun bayanan sirri akan makarantar.

An kwace motoci, layoyi, wayoyi da sauransu

An samu bayani akan yadda Samad, dan damfarar yanar gizo ya bude makarantar a gida mai dakuna 3 ya na koyar da matasa yadda ake damfarar jama’a a gidan da ya ke biyan N3m a matsayin kudin hayar ko wacce shekara.

Hukumar ta sanar a takarda ranar Alhamis, a lokacin da aka kama su cewa an samu nasarar kwace motocin hawa kirar Lexus SUV da Toyota Highlander; na’urori masu kwakwalwa, wayoyi, layu da sauransu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Sannan an samu bayani akan yadda wadanda aka kama su ka yi wa jami’an bayanai masu amfani wadanda za a yi amfani da su a kotu da zarar an kammala bincike.

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

A wani labarin, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164