Mun rufe kwalejin ilmin Shehu Shagari bisa kisan daliba, kowa ya koma gida: Hukumar makarantar

Mun rufe kwalejin ilmin Shehu Shagari bisa kisan daliba, kowa ya koma gida: Hukumar makarantar

  • Hukumomi a kwalejin lmin Shehu Shagari sun umurci dukkan daliban makarantar su koma gida
  • Jawabi ya nuna cewa an rufe kwalejin ilmin har ila ma sha'aLLahu sakamakon abinda ya faru da safe
  • An kashe wata dalibar kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi

Sokoto - Hukumar kwalejin ilmi ta Shehu Shagari dake jihar Sokoto, Arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da rufe makarantar bisa abinda ya auku da safiyar Alhamis.

Kwalejin, a jawabin da ta saki da rana ta bayyana cewa sakamakon abinda ya faru da safiyar Alhamis, an rufe makarantar kuma dalibai su koma gida.

A jawabin da Legit ta gani a Tuwita, an ce dukkan dalibai suyi gaggawan komawa gida.

A cewar jawabin:

"Sakamakon rikicin dalibai da safiyar nan a kwalehin, hukumomin kwalejin sun yanke shawarar rufe makarantar har sai baba ta gani."

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

"Bayan haka, ana umurtan dukkan dalibai su koma gida cikin gaggawa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar makarantar
Mun rufe kwalejin ilmin Shehu Shagari bisa kisan daliba, kowa ya koma gida: Hukumar makarantar Hoto: @GanzyMalgwi
Asali: Twitter

Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi

Mun kawo muku cewa an kashe wata dalibar kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi)

21stCC ta ruwaito cewa an kashe dalibar mai suna Deborah bayan an bukaci ta janye kalamanta amma taki.

Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe.

Bidiyoyi a kafafen sada zumunta sun nuna yadda dalibai suka yiwa dalibar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng