Da Dumi-Dumi: Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu mutane su yi murabus

Da Dumi-Dumi: Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu mutane su yi murabus

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci gwamnan CBN ya yi murabus daga kujerarsa idan zai nemi takara
  • Bayan umarnin ministoci, wata takarda da Sakataren gwamnati ya fitar ta tattaro dukkan masu rike da muƙamai da lamarin ya shafa
  • Zuwa yanzu ministoci uku cikin Tara da abun ya shafa sun yi murabus daga kan mukaman su

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci, shugabannin hukumomi, sanssan ma'aikatu, jakadun Najeriya da sauran naɗe-naɗe da ke da niyyar siyasa su yi murabus.

A wata takarda da jaridar Punch ta gani ranar Alhamis da safe, wakilin jaridar ya gano cewa ofishin gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da sauran hukumomin gwamnati duk sun shiga ciki.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Da Dumi-Dumi: Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu mutane su yi murabus Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Takardar mai lamba SGF/OP/ I/S.3/XII/ 173 na ɗauke da sa hannun Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Wani sashin takardar da SGF ya fitar ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Domin share tantama, wannan umarnin ya shafi ma'aikatu, shugabanni da mambobin sassan ma'aikatu, hukumomin gwamnatin tarayya, jakadu da sauran naɗe-naɗen FG waɗan da ke da kudirin neman takara."

Channels tv ta ruwaito cewa SGF ya yi bayanin cewa duk wanda umarnin ya shafa ya miƙa ragamar wurin da yake hannun babban ma'aikacin da ke kusa da shi.

Buhari ya ba su wa'adin kwana 5

Tun farko dai, shugaban ƙasa Buhari ya umarci mambobin majalisar zartarwa da ke da niyyar tsayawa takara su aje aikin su.

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, wanda ya tabbatar da haka jim kaɗan bayan taron FEC, yace duk waɗan sa abun ya shafa an ba su wa'adin daga nan zuwa 16 ga watan Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Minitoci tara ne abun ya shafa waɗan da ke neman takarar wata kujerar siyasa da zaɓen 2023 da ke tafe.

Ƙaramin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, shi ne na farko da ya fara murabus bayan umarnin Buhari, daga bisani ministan kimiyya da fasaha da ministan harkokin Neja Delta suka biyo baya.

A wani labarin kuma Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana sunan ɗan takarar da yake rokon Allah ya gaji Buhari a 2023

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nuna goyon bayansa ga Yemi Osinbajo a zaɓen 2023.

Malamin ya ce ya jima ya na wa mataimakin shugaban Addu'a don haka zai nunka rokon Allah ya samu nasara a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262