Da Dumi-Dumi: Ministan kimiyya da fasaha ya yi murabus daga gwamnatin Buhari
- Bayan umarnin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, har an sami ministoci biyu sun yi murabus daga kan muƙamansu
- Ministan kimiyya da fasaha, Mista Ogbonnaya Onu, ya bi sahun karamin ministan ilimi, ya yi murabus daga kujerarsa
- A ranar 6 ga watan Mayu, 2022, Onu ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki
Abuja - Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya bi umarnin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi murabus daga mukaminsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Shugaba Buhari ya umarci duk wani mamban majalisar zartarwa na gwamnatinsa da ke neman wata kujerar siyasa ya yi murabus ranar ko kafin 16 ga watan Mayu, 2022.
An sanar da umarnin ne a wurin taron majalisar zatarwa na yau Laraba, 11 ga watan Mayu 2022 wanda ya gudana bisa jagorancin shugaban ƙasan a Aso Villa.
Wasu majiyoyi ma su karfi a cikin ofishin Sakataren gwamnatin tarayya da kuma ma'aikatar kimiyya da fasaha sun tabbatar da cewa ministan ya aje aikinsa.
Ɗaya daga cikin majiyar ta ce:
"Ministan ya je ofishin SGF domin miƙa takardar aje aiki, kuma dama haka ake tsammani kasancewar shugaban ƙasa ya umarci su yi murabus."
Wace takara Ministan zai nema a 2023?
A ranar 6 ga watan Mayu, 2022 ne Mista Onu ya ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen da ke tafe.
Ministan ya bi sahun ƙaramin ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, wanda shugaban ƙasa Buhari ya sanar da murabus ɗinsa wurin taron FEC ranar Laraba.
A wani labarin kuma Kwankwaso ya bayyana cewa kofar NNPP abuɗe take da kowane ɗan Najeriya har wanda ba su shiri
Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kofar shigowa jam'iyyar su a buɗe take ga kowa.
Tsohon gwamnan Kano ya ce sun kafa jam'iyyar NNPP ba ga makusanta kaɗai ba, kowa ya na da dama har da wanda ba su shiri.
Asali: Legit.ng