Kebbi: Hukumar yan sanda ta miƙa cakin Miliyan N60m ga iyalan yan sanda 6 da yan bindiga suka kashe

Kebbi: Hukumar yan sanda ta miƙa cakin Miliyan N60m ga iyalan yan sanda 6 da yan bindiga suka kashe

  • Hukumar yan sanda ta jihar Kebbi ta gabatar da cakin zunzurutun kuɗi miliyan N60m ga iyalan yan sanda 6 da suka mutu a bakin aiki
  • A ranar 15 ga watan Maris, yan sandan suka rasa rayuwarsu yayin fafatawa da yan bindiga yayin a kamfanin GB Food Company
  • Iyalan sun nuna matukar jin daɗin su tare da yabo ga kwamishinan yan sanda da kamfanin bisa abinda suka kira karamci

Kebbi - Hukumar yan sandan jihar Kebbi a ranar Talata, ta gabatar da Cakin kudi miliyan N60m ga iyalan yan sanda shida, waɗan da yan bindiga suka kashe a bakin aiki.

Yan sandan sun rasa rayukansu a wani gumurzu da yan bindiga yayin da suke aikin gadi a kamfanin GB Food Company da ke kauyen Gafara, karamar hukumar Ngaski jihar Kebbi, ranar 15 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Yan sanda sun mika kudi da iyalan waɗan da aka kashe a bakin aiki.
Kebbi: Hukumar yan sanda ta miƙa cakin Miliyan N60m ga iyalan yan sanda 6 da yan bindiga suka kashe Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta rahoto cewa Kakakin hukumar yan sanda jihar, SP Nafi’u Abubakar, shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, ranar Talata.

Kakakin ya ce kwamishinan yan sanda, CP Musa Baba, ne ya gabatar da Cakin kudin ga iyalan mamatan a madadin kamfanin GB Food Company.

Ya ce:

"An damƙa Cakin naira miliyan N60m ga iyalan yan sandan da suka rasu kuma kowane gida ya samu Naira miliyan N10m."
"Halin karamcin da Kamfanin ya nuna ba ya tsaya iya tallafawa iyalan mamatan yan sandan bane kaɗai, har da kara wa dakarun yan sanda da ke aiki kwarin guiwar su ƙara zage dantse wajen yaƙi da ta'addanci."

Kwamishinan yan sandan ya shawarci iyalan su bi a hankali da tsantsaini wajen amfani da tallafin a ɓangaren bukatun su na kudi.

Kara karanta wannan

Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana

Iyalan sun yi godiya da karamci

Da yake jawabi a madadin iyalan yan sandan shida, Fafa Ijantiku, ya yaba da karamcin kwamishinan yan sanda da kuma kamfanin.

Ya ƙara da Addu'ar Allah ya cigaba da ba su kariya a dukkan harkokin da suka sanya a gaba na yau da kullum.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun gindaya sharuddan zaman lafiya a jihar Sokoto

Tsagerun yan bindiga sun sake kai hari kan mutanen gari a yankin ƙaramar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto.

Mazauna ƙauyen sun yi kokarin tarbar maharan har suka kashe musu mutum uku, hakan ya fusata yan ta'addan suka kashe 8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262