Mutanen Gari Sun 'Tarwatse' Sun Shiga Daji Bayan Da 'Yan Bindiga Suka Kai Hari a Neja

Mutanen Gari Sun 'Tarwatse' Sun Shiga Daji Bayan Da 'Yan Bindiga Suka Kai Hari a Neja

  • Rahotanni sun nuna yadda mazauna wasu garuruwa uku da ke karamar hukumar Munya a cikin Jihar Neja su ka tsere daji yayin da ‘yan bindiga su ka kai musu hari
  • An samu bayanai akan yadda ‘yan bindiga su ka kai hari Dandaudu, Gidan Mangoro da Gini da misalin karfe 2:30 na ranar Litinin
  • Wani jagoran na jam’iyyar PDP a Munya ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shiga kauyen ne ta babban titin Sarkin Pawa wanda ya hada Jihar Kaduna da Neja

Neja - Yayin da ‘yan bindiga su ka kai hari wasu garuruwa da ke karamar hukumar Munya inda mazauna yankin sun yi ta tserewa daji, The Cable ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda ranar Litinin su ka kai harin kauyen Dandaudu, Gidan Mangoro da Gini da misalin karfe 2:30 na rana.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Mutanen Gari Sun 'Tarwatse' Sun Shiga Daji Bayan Da 'Yan Bindiga Suka Kai Hari a Neja
Mutanen Gari Sun Shiga Daji Bayan Da 'Yan Bindiga Suka Kai Hari a Neja. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Yayin tattaunawa da wakilin The Cable ta wayar salula, Dantala Noma, wanda jagora ne na jam’iyyar PDP a Munya, ya ce ‘yan bindigan sun shiga kauyen ne ta babban titin Sarkin Pawa wanda ya hada Jihar Neja da Kaduna.

Sun yi garkuwa da akalla mutane 3

A cewarsa, ‘yan bindigan sun kai dare su na ta kai farmaki wuri-wuri inda su ka yi garkuwa da akalla mutane 3 sannan su ka sace shanu da dama.

A cewarsa:

“Garinmu yana cikin damuwa. Da farko sun afka kauyen Dandaudu kafin su nufi wani kauyen a karamar hukumar Munya.
“Ba su shigo ta daji ba; sun yi amfani da babban titin Sarkin Pawa ne. A baburansu suka shigo inda su ka dinga kai hare-hare a titina kafin su shiga kauyaku.

Kara karanta wannan

An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

“Har karfe 10 na dare su na kai hari. Sun kwashe shanu da dama sannan aka sace wasu daga kauyakun sannan su ka yi garkuwa da mutane 3 daga wurare daban-daban.”

Ya bayyana yadda su ka sace wani Usman daga Unguwan Mangoro sannan su ka sace wasu mutane biyu daga Dandaudu da Gini wadanda yanzu haka su na hannunsu.

Ya ce ko jami’in tsaro daya ba su gani ba. Har a Maraban Dandaudu inda a baya jami’an tsaro su ke zama, duk an kwashe su. Babu wanda ya san dalilin hakan. Hakan ya sa mutane su ka dinga guduwa daji.

Garba Mohammed, shugaban karamar hukumar Munya, ya tabbatar da harin inda ya ce ‘yan bindigan sun halaka wani Bafulatani wanda su ka kwace wa shanu.

Ya ce har safiyar Talata su na kokarin fitar da shanun da su ka sace

A cewarsa:

“Mun samu labarin yadda su ka taru wurin Kampana. Na sanar da kwamishinan kananun hukumomi kuma sun tabbatar mana da cewa za su tura sojoji don mun ji babu su a wurin hakan ya sa ‘yan ta’addan su ka afka kauyen Dandaudu.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

“Sun sace kayan abinci sannan sun halaka wani Bafulatani bayan kwace masa shanunsa. Yanzu da na ke maka magana su na cikin kauyen su na kokarin fitar da shanun.”

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164