An gurfanar da faston da ya nemi mabiyansa su biya N300,000 kudin shiga aljannah
- Kotu a jihar Ekiti ta bayar da belin wani malamin addini da ya so damfarar mabiyansa, Fasto Noah Abraham Adelegan
- Fasto Abraham dai ya nemi mabiyansa su biya kudi N310,000 domin shiga aljannah bayan ya ce masu ya san hanyar da ake bi a shige ta
- Mai shari’a Titilola Olaolorun ta bayar da belin wanda ake karar a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa
Ekiti - Wata kotun majistare ta jihar Ekiti da ke zama a Ado-Ekiti ta bayar da belin Fasto Noah Abraham Adelegan na cocin Christ High Commission Ministry, Omuo Oke-Ekiti.
Fasto Abraham shine malamin addini wanda ya fada ma mabiyansa cewa yana iya kai su aljannah, yana mai cewa Omuo-Ekiti ne kofar shiga aljannah, Daily Trust ta rahoto.
Sannan ya kuma bukaci mabiyan nasa da su biya N310,000 kafin su samu damar shiga aljannah.
Tuhumar da ake masa ya zo kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Cewa kai Fasto Noah Abraham Adelegan a ranar 27 ga watan Afrilu, a Omuo Oke-Ekiti a yankin Omuo, ta hanyar karya da niyar zamba, ka gabatar da kanka ga taron jama’a a cocin Christ High Commission Ministry, Omuo, Oke-Ekiti, a matsayin wanda zai iya kaisu aljannah kafin tashin duniya idan suka biya kudi daga N300,000 zuwa N310,000 kwannensu.”
Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Johnson Okunade, ya ce laifin ya saba wa sashe na 416 na dokar laifuka ta jihar Ekiti na shekarar 2012.
Lauyan wanda ake kara, Adunni Olanipekun, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa, inda ya kara da cewa a shirye yake ya gabatar da amintattun wadanda za su tsaya masa.
Sufeto Okunade bai yi adawa da bukatar ba amma ya bukaci kotun da ta yi amfani da damar ta wajen bayar da belin ko kuma kin amincewa da shi, jaridar The Sun ta rahoto.
Alkalin kotun mai shari’a Titilola Olaolorun ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Mayu.
Jama'ar gari sun kadu da ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su
A wani labarin, mazauna garin Takakume a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto sun kadu a ranar Lahadi lokacin da suka gano cewa tsohon makwabcinsu ne shugaban yan bindigar da suka farmake su.
Yan bindiga dauke da makamai sun farmaki garin a safiyar ranar Lahadi, amma sai yan banga suka yi musayar wuta da su, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar shugaban yan ta’addan, rahoton Daily Trust.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban karamar hukumar, Abdulwahab Goronyo, ya ce yan bindigar sun farmaki garin da tsakar dare, suka kashe mutum daya tare da sace wasu shida.
Asali: Legit.ng