Da duminsa: Majalisar zartarwa ta ASUU na tattaunawa, ta yuwu a kara wa'adin yajin aiki
- Majalisar zartarwa ta kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'in Najeriya sun shiga tattaunawa da yammacin nan
- Daya daga cikin mambobin majalisar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya sanar da cewa ta yuwu su kara wa'adin yajin aiki
- A ranar Juma'a da ta gabata, ministan kwadago da aikin yi, Dr Chris Ngige ya sanar da cewa gwamnati za ta cigaba da sasanci da ASUU
Mambobin majalisar zartarwa ta Kungiyar Malamai masu Koyarwa ta Jami'o'in Najeriya a halin yanzu sun shiga ganawa, jaridar Punch ta gano hakan.
Wani mamban majalisar zartarwar ya sanarwa da Punch cewa ta yuwu a kara wa'adin yajin aikin duba da abinda ake tattaunawa a cikin taron yanzu.
A ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, Kungiyar Malamai masu Koyarwa ta jami'o'in Najeriya suka shiga yajin aikin jan kunne domin assasa biyan wasu bukatunsa daga gwamnatin tarayya.
Malaman jami'o'in sun bukaci gwamnati da ta tabbatar da yarjejeniya da suka saka hannu a watan Disamban 2020 kan kudin da za a fitar wurin farfado da jami'o'in gwamnati.
Sauran bukatun Malaman sun hada da biyansu alawus din su, sake sasantawa kan yarjejeniyar 2009 da kuma amfani da tsarin biyan albashi da fasahar UTAS da sauransu.
A daya bangaren, ministan kwadago da aikin yi, Dr Chris Ngige, a ranar Juma'a ya sanar da cewa gwamnatin tarayya da ASUU za su cigaba da tattaunawa a cikin makon nan.
Bayan Kwashe kwanaki 56 ana yajin aiki, Gwamnatin Buhari zata gana da ASUU
A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta hannun ministan Kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ta shirya zama da kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU, yau Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022.
Punch ta rahoto cewa taron wanda aka shirya farawa da misalim ƙarfe 5:00 na yamma, zai samu halartar wakilan gwamnati da kuma na ASUU.
Daraktan watsa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar kwadugo ta ƙasa, Patience Onuobia, a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, ta ce Ngige ne zai jagoranci taron da kansa.
Asali: Legit.ng