Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari, Janar Buba Marwa

Shugaban hukumar hana fataucin muggan kwaya, NDLEA, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa, ya bayyana cewa hukumarsa zata kwace dukiya duk wandaaka kama kwayoyi kuma za'a rufe akawunt dinsa.

Marwa ya bayyana hakan ne a hirarsa da VOA Hausa kuma Legit ta kallo a Kaduna.

A cewarsa, harkar safarar kwayoyi na da kudi da yawa ciki saboda haka ko an jefa mutum kurkuku ba'a kwace kudin ba, zai fito ya cigaba daga inda ya tsaya.

Yace:

"Cikin lamarin shaye-shaye da fataucinsu, akwai dimbin kudi a wannan harkar. Abin kadan za'a ga kudi da yawa."
"Sai muka lura wasu basu damu ba a kamasu, a gurfanar da su a kotu, a kaisu kurkuku. Ko shekara 5 ko 10 ne, saboda zasu fito dukiyar na nan. Saboda haka zamu bi mutum da dukiyarsa."

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

"Wannan ba kan Abba Kyari kadai ne ba. Haka aikinmu yake, duk wanda muka kama shima dukiyashi zamu rufe, akawunt dinshi zamu rufe, duk kudin da ya samu sakamakon wannan harkar duk zamu kama."

Kalli hirar a nan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel