Bayan tattaki daga Gombe zuwa Legas don Tinubu, matashin zai koma gida bai ga Tinubu ba

Bayan tattaki daga Gombe zuwa Legas don Tinubu, matashin zai koma gida bai ga Tinubu ba

  • Wani mutumi da yayi tattaki daga jihar Gombe zuwa Legas don nuna goyon bayansa ga Tinubu zai koma gida bai gansa ba
  • Aminu Abdulmumini Jor, wanda mai gyaran takalmi ne ya ce zai koma bakin aikinsa a garin Gombe
  • Aminu ya so ganawa da jigon APCn amma yace babu matsala har yanzu yana son Tinubu kuma yana goyon bayansa

Wani matashi dan jihar Gombe, Aminu Abdulmumini Jor, wanda yayi tattaki daga jihar Gombe zuwa Legas don nuna goyon bayansa ga Asiwaju Bola Tinubu ya shiga rudani bayan kwashe 25 a Legas har yanzu bai ga Tinubu ba, The Sun ta ruwaito.

An tattaro cewa Aminu yanzu haka ya garzaya Abuja bayan rashin samun ganin jigon na APC.

Yayin hira da jaridar, Aminu yace ko a jikinsa rashin samun haduwa da Asiwaju Bola Tinubu don bayyana masa son da yake masa.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Ya ce yana goyon bayan Tinubu ne saboda dattijo ne kuma ya dadde yana goyon bayan Arewa.

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Goyon bayan da ya yiwa Buhari a 2015 ya isa kowani dan Arewa ya goyi bayan mutumin (Tinubu), shi yasa nayi tattaki daga Gombe zuwa Legas don nuna masa goyon baya na."

Aminu Jor
Bayan tattaki daga Gombe zuwa Legas don Tinubu, matashin zai koma gida bai ga Tinubu ba Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Aminu yace kalaman da mutane ke masa ba dadi

Yayinda bayyana abubuwan da ya fuskanta, ya ce mutane da dama sun yi masa kalamai mara dadi yayinda ya bayyana niyyar tattakin.

Yace wasu ma cewa sukayi Allah ya hada shi da masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shi cikin daji.

Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai

Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ido hudu da maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Manyan jigogin APCn biyu sun hadu ne a taron zaman hadin kai tsakanin yan takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC daga yankin kabilar Yoruba.

Dattawan yankin kudu maso yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda za'a hada kai da juna don tsayar da mutum guda cikinsu.

Dattawan sun hada da tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, da tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel