Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau na shagalin Sallah a Kasar waje
- Jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta fito fes cikin kyakkyawar shiga domin murnar zuwan ƙaramar Sallah (Eid-El-Fitr).
- Ramaha Sadau, wacce alamu suka nuna ta yi shagalin Sallah a kasar waje, ta yi wankan bakar Abaya da Mayafi baki
- A ranar Litinin 2 ga watan Mayu, 2022, al'ummar Musulmai a Najeriya da wasu ƙasashe suka gudanar da Sallar Idi bayan cika Azumi 30
Jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Rahama Sadau, ta fito fes cikin kyakkywar shiga domin murnar zuwan ƙaramar Sallah (Eid-El-Fitr) bayan kammala azumin Ramadan.
Jarumar ta yi shigar baƙar Abaya da kuma mayafi wanda shi ma baki ne yayin da ta turo hutunan Sallah a shafinta na dandalin sada zumunta wato Instagram.
Wurin da Jarumar ta ɗauki Hotunan ya nuna cewa ba'a gida Najeriya bane ba kuma ta watsa Hotunan domin masoyanta.
Hotunan Rahama Sadau
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Litinin 2 ga watan Mayu, 2022, al'ummar Musulmai a faɗin Najeriya suka gudanar karamar Sallah bayan kammala ibadar Azumin watan Ramadan.
Watan mai albarka da gafara, wanda Musulman duniya ke kamewa daga ci ko sha ko kusantar iyali tun daga hudowar rana zuwa faɗuwarta, ya cika kwana 30 cif a bana.
Jaruma Rahama Sadau, wacce take mabiya addinin Musulunci ta bi sahun yan uwanta Musulman duniya wajen murnar Sallah karama.
A wani labarin na daban kuma Jarumi Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano
Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, yan Najeriya dake da niyyar tsayawa takara na cigaba da faɗa wa duniya aniyarsu.
A masana'antar Kannywood, Jarumi Lukman na Labari na ya bayyana tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya daga Kano.
Asali: Legit.ng