Yanzu-yanzu: Tsagin Ganduje ya yi nasara a kotun koli, an yi watsi da su Shekarau
- Kotun Allah ya isa ta raba gardama tsakanin tsagin gwamna Abdullahi Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau
- Bayan nasara a kotun daukaka kara a baya, kotun koli ta tabbatar da sihhancin Abdullahi Abbas matsayin shugaban APC na Kano
- Rikici ya barke tsakanin Ganduje da Shekarau ne bayan zaben shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano
FCT, Abuja - Kotun Koli dake Abuja ta yi watsi da Shari'ar da tsàgin Malam Ibrahim Shekarau suka kai suna qalubalantar Shugabancin Jamiyyar APC ta Jihar Kano ta tsagin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.
A shari'ar da kwamitin Alkalan kotun koli biyar karkashin Alkai Inyang Okoro, suka yanke ranar Juma'a, sun yi ittifakin cewa shari'ar da kotun afil tayi a baya babu gaskiya ciki, rahoton DailyTrust.
Yan banza bakwai dama karya suka shuka: Cewar Ganduje bayan nasara a kotun daukaka kara
Gabanin zuwa kotun koli, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano a tsakiyar manyan jami'an gwamnati da hadimansa a gidan hutun jihar Kano dake unguwar Asokoro Abuja, Ganduje ya bayyana godiyara bisa al'ummar Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa,
"Muna gode wa al'ummar jihar Kano, muna godewa yan jam'iyyar APC...Muna gode wa shugaban riko na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe saboda shi yace mu koma kotu ."
Gwamna Ganduje ya kara da cewa yan tsagin tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau watau G7 dusa suka shuka saboda haka ba zasu girbe 'yaya ba.
Asali: Legit.ng