Idan kuka zabe ni, zan yi yaki da rashawa kamar yadda Buhari ke yi: Godswill Akpabio
- Daya daga cikin ministocin Buhari ya yi alkawarin cigaba daga inda maigidansa ya tsaya wajen yaki da rashawa
- Akpabio ya shiga jerin ministocin gwamnatin shugaba Buhari dake neman takara kujeran shugaban kasa
- Akpabio ya ce Shugaba Buhari na yaki da rashawa yadda ya kamata
Abuja - Ministan harkokin yakin Neja Delta, Godswill Akpabio, a ranar Alhamis ya ce zai cigaba da yaki da rashawa kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke yi idan aka zabesa a 2023.
Akpabio, ya shiga jerin masu neman kujerarn shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jawabi yayin hira a shirin PoliticsToday na ChannelsTV, Ministan ya yabawa yaki da rashawan da gwamnatin Buhari ke yi.
A cewarsa:
"Wajibi ne mu cigaba da yaki da rashawa saboda idan ba haka ba, rashawa za ta kashemu. Zan cigaba daga inda Shugaban kasa ya tsaya."
'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya
"Abinda yake yi shine yakin rashawa da talauci. Ba zamu iya yaki da rashawa ba tare da mun yaki talauci ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Akpabio, wanda tsohon gwamnan Akwa Ibom ne kuma tsohon Sanata ya ce abubuwa uku manyan matsalolin kasar nan.
A cewarsa sune, matsalar tsaro, rashin hadin kan yan kasa da kuma tattalin arziki.
Ya ce idan yan Najeriya sun zabesa a zaben 2023, zan magance wadannan matsalolin.
Binciken NDDC: Sai an amayo dukkan kuɗaɗen da aka sace, babu sisin kwabo da za mu ƙyalle, Buhari
A wani labarin kuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu kwabon da zai yi kuka, bayan kammala binciken kudaden Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta, NDDC, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasar ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabi ta yanar gizo a taron kaddamarwar samfurin dakunan NDDC a jami’ar Uyo da ke Akwa Ibom.
Buhari ya ce an kammala kididdigar kuma an gano inda ko wanne kwabo ya sake yayin da ko wanne mai laifi zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.
Asali: Legit.ng