UTME 2022: Muhimman abubuwan da ya kamata kowane ɗalibi ya sani game da JAMB
A gobe idan Allah ya kaimu za'a fara jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da Sakandire (UTME) da hukumar JAMB ke shirya wa duk shekara.
Premium Times ta rahoto cewa za'a fara zana jarabawar ne gobe Jumu'a 6 ga watan Mayu, 2022 a faɗin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.
UTME wacce ake gudanarwa a na'ura mai ƙwaƙwalwa (CBT) ta kasance wani shinge tsakanin ɗaliban da suka kammala Sakandire dake neman takardar izinin shiga makarantun gaba a Najeriya.
Sama da ɗalibai miliyan ɗaya da rabi ke zana jarabawar duk shekara, amma a bana JAMB tace sama da 1,837,011 sun yi rijsta domin zama jarabawar ta 2022.
JAMB tace ta gama shiri cikin nasara a dukkan cibiyoyi 750 a faɗin kasar nan, sannan ta jero abubuwan da ta halasta da wanda ta haramta wa ɗalibai yayin jarabawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta gargaɗi cewa ba zata lamurci gaza kiyaye waɗan nan dokoki ba, inda JAMB ta ce:
"Kowane mai zana jarabawa ya sani ba bu wata jarabawa da za'a sake mata ranar rubutawa kan koma wane dalili ne."
Legit.ng Hausa ta tattaro muku abubuwan da ya dace ku sani. Ga su kamar haka:
Sake fitar da Silif ɗin JAMB
JAMB ta sanar da cewa jarabawar bana zata gudana ne tsakanin Jumu'a 6 ga watan Mayu zuwa Asabar 14 ga Mayu, 2022, bisa haka ts umarci kowane ɗalibi ya sake fitar da Silif daga ranar 30 ga watan Afrilu.
A cewar hukumar ta haka ne kaɗai ɗalibi zai san cikakken bayani kan Cibiya, da ranar da zai zauna ta shi jarabawar.
Gano cibiyar da zaka yi jarabawa
Domin kiyaye samun matsala, JAMB ta shawarci dalibai su nemi cibiyar da aka tura su tun kafin ranar jarabawa domin saukaka musu gano ainihin ranar da zasu halarci wurin.
Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi
Hakanan ta shawarci kowane ɗalibi ya tabbatar ya halarci wurin da aka tura shi tun kafin lokacin da zai shiga jarabawa.
Abubuwan da aka hana shiga da su
Hukumar dake shirya jarabawan ta ƙara jaddada cewa duk wani abu musamman mai amfani da wuta ta haramta zuwa da shi harabar cibiyar zana jarabawa.
JAMB ta lissafa irin waɗan nan abubuwa da ta hana shiga da su, da suka haɗa da, wayoyin hannu, Agogon hannu, Biro, na'urar lissafi, da makamantan su. Da kuma USB, Sidi da sauran kayan ajiya.
Sauran abubuwan sun haɗa da, littafi da sauran kayan karatu, Kamara, kayan naɗan sauti, Makirfo, abun sauti, Bulutuz, sarƙa, makullai, Katin ATM, kyallen hannu, takardun kuɗi da abun goge rubutu.
Ta ƙara da cewa ba'a bukatar mutum ya zo da gilashi hakanan na gayu. Sai dai Gilashin ƙara gani ga wanda ke da lalurar jami'ai zasu bincika shi kafin ka shiga.
Binciken shatin yatsa kafin shiga jarabawa
JAMB ta jaddada cewa ba zata amince da duk wata hanyar tabbatarwa ba in banda ta zanen yatsan hannu, wanda a cewarta ta kara haɓaka shi don saukaƙa wa dalibai.
Hukumar ta ce kowane ɗalibi sai ya dangwala hannunsa ya ɗauka kafin ya shiga, kuma ma'aikata ba zasu ɓata lokaci kan mutum ɗaya ba idan har ya ƙi ɗauka bagan wasu yunkuri.
A cewar JAMB, wannan hanyar ce kaɗai zata yi rijista da tabbatar da cewa ɗalibi ya halarci wurin domin rubuta jarabawarsa.
A wani labarin na daban kuma Kan wasu dalilai, wani Sanatan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
Sanata Ibikunle Amosun, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe.
Tsohon gwamna a jihar Ogun ya ce yana da faɗin kwarewa a kowane ɓangare da mataki na gwamnati kuma ya shirya yi wa ƙasa aiki.
Asali: Legit.ng