Magidanci ya lakaɗa wa matarsa dukan tsiya, ya yi barazanar kasheta kan ta cika kwalliya
- Yan sanda a Legas sun gurfanar da wani Magidanci gaban Kotu kan zargin barazanar kashe matarsa
- Ana tuhumar Magidancin da lakaɗawa matarsa dukan tsiya da kuma faɗa mata zai ga bayanta kan yawan amfani da Make-Up
- Kotu ta ba da Belin mutumin kan kuɗi N50,000 da mutum biyu da zasu tsaya masa, an ɗage sauraron ƙara
Lagos - Hukumar yan sanda a jihar Legas ta gurfanar da wani Magidanci ɗan shekara 48, Emmanuel Amamchukwu, gaban Kotun Majistire bisa zarge-zarge guda huɗu.
Daily Trust ta rahoto cewa yan sandan suna zargin Magidanci da cin mutuncin matarsa da kuma barazanar kashe ta kan tana yawan kwalliya da suke kira 'Make-Up.'
Yan sanda na tuhumar Amamchukwu da aikata abubuwa huɗu, cin mutunci, tsoratarwa, gaza sauke nauyi, da kuma barazanar kisa.
Mai shigar da ƙara, ASP Cousin Adams, ya shaida wa Kotun cewa mutumin da ake zargin ya aikata laifin a ranar 1 ga watan Mayu, a gida mai lamba 1, layin Ondo a Ebute Meta.
Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi
ASP Adams ya faɗa wa Kotun cewa Magidancin ya yi barazanar kashe matarsa, Chinelo, bayan ya lakaɗa mata dukan tsiya kuma ya raunata ta a Fuska saboda tana amfani da Make-Up.
Ya kara da cewa Mutumin ya gaza sauke nauyin dake kansa a matsayin shugaban iyalansa, maimakon haka ya zama barazana ga zaman lafiyar gidan.
Wane mataki Kotun ta ɗauka kan mutumin?
Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Misis F.F. George, ya amince da ba da belin wanda ake zargi kan N50,000 da kuma mutum biyu da zasu tsaya masa.
Daga nan kuma sai ta sanar ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Yuni, 2022, sannan za'a dawo don cigaba.
A wani labarin na daban kuma Wata nakiya ta sake fashewa da mutane, rayuka sun salwanta
Wani abun fashewa da ya ƙara tashi kusa da Kamfanin Man Fetur ya yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Imo.
Bayanai sun nuna cewa mutum biyun na kan hanyar da ta nufi kamfanin lokacin da abun ya fashe suka mutu nan take.
Asali: Legit.ng