Gwamna Abdullahi Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 90 Afuwa a Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 90 Afuwa a Kano

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya yi wa fursunoni 90 afuwa a gidajen gyaran hali na Kano
  • Abba Anwar, kakakin gwamnan na Kano ne ya sanar da hakan yana mai cewa afuwar karamci ne da aka yi yayin bikin Sallah
  • Anwar ya ce gwamnatin Kano ta bukaci fursunonin da aka yi wa afuwar su tafi gidan gwamnati su yi rajisan koyon sana'o'i

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa fursunoni 90 afuwa a gidajen gyaran hali daban-daban da ke jihar, Premium Times ta rahoto.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya yi wa fursunonin afuwan ne yayin ziyarar bikin Sallah da ya kai Goron Dutse a Kano, ranar Litinin tare da wasu mambobin SEC a Jihar da shugabannin jam'iyya da manyan jami'an gwamnati.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Gwamna Abdullahi Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 90 Afuwa a Kano
Sallah: Gwamna Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 90 Afuwa a Kano. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Gwamnan, a cewar sanarwar da kakinsa, Abba Anwar, ya fitar ya bukaci fursunonin da aka yi wa afuwa su taho gidan gwamnati su yi rajistan koyon sana'a, ya kuma bada tabbacin cewa, za a yi wa wasu fursunonin 70 afuwa yayin bikin sallah.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"An yi wa wasu daga cikin ku afuwa ne saboda rashin lafiya, wasu kuma saboda shekaru, wasu saboda rashin iya biyan tara da aka ci ku; wasu ma an yanke musu hukuncin kisa.
"Duk da cewa an koyar da su wasu sana'o'i, wasu da ke bukatar karin koyon sana'ar su garzaya gidan gwamnati nan take su yi rajista domin wani koyon sana'an."

Gwamnan ya tunatar da su cewa ba an yi musu afuwar bane kawai domin rage cinkoso a gidajen gyaran halin, amma saboda a sake basu wata damar su canja halayensu zuwa masu kyau.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Sallah: Wamakko Ya Biya Wa Fursunoni 50 Bashi Da Tara, Za Su Tafi Gida Su YI Sallah Da Iyalansu

A wani rahoton, Sanata Aliyu Wamakko, mai wakiltan Sokoto ta arewa ya kubutar da fursunonin gidan yari su 50 daga gidan gyaran hali na Sokoto, rahoton Daily Nigerian.

An saki fursunonin ne bayan Wamakko ya biya musu tara da basusuka da ake bin su.

Yayin da ya ke sakin fursunonin, Jami'in walwala a gidan gyaran hali na Sokoto, ASP Ayyuba Alhassan, ya yaba wa Wamakko saboda cigaba da wannan karamcin duk shekara.

Mai magana da yawun Wamakko, Hassan Sanyinnawal, a ranar Laraba a Sokoto ya ce cikin mutanen 50 da aka samawa yanci guda shida mata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel