Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai Makka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da yunkurin hari da yan ta’adda suka kai kasa mai sarki, garin Makka a karshen mako.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, shugaban kasa Buhari yayi Magana da sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud na kasar Saudiyya don nuna jimamin kasar Najeriya tare da Sarkin bayan yan bindigan Houthi sun kai kaddamar da wani hari a kasa mai tsarki.
Buhari yayi Allah wadai da aikin wanda aka kai akan mutanen da basu san hawa ba, a matsayin abun kunya da wulakanci.
Ya kuma nuna yabawa kan cewa jami’an tsaron Saudiyya sun cimma yan ta’addan daga tsawon kilomita 65 daga garin Makka.
KU KARANTA KUMA: Talauci ke haddasa sace-sacen mutane, ta’addanci- Dangote
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, a ganawar da sukayi na wayar tarho tare da sarkin, shugaban kasa Buhari ya bayyana bukatar a kara taimakon kasa da kasa don suyi yaki a kan ta’addanci da kuma yawan rikici.
A halin yanzu, shugabannin Niger Delta da manyan masu ruwa da tsaki sun ki amincewa da shirin zuba jarin dala biliyan 10 (naira triliyan 4) na gwamnatin shugaban kasa Buhari.
Wannan bayanin yazo ne a lokacin da ake sa ran shugabannin Niger Delta zasu hadu tare da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng