Abinda Yasa Muka Fille Wa Soja Da Matarsa Kai a Hanyarsu Na Zuwa Ɗaurin Aurensu, Ɗaya Cikin Makasan Ya Magantu

Abinda Yasa Muka Fille Wa Soja Da Matarsa Kai a Hanyarsu Na Zuwa Ɗaurin Aurensu, Ɗaya Cikin Makasan Ya Magantu

  • Daya daga cikin ‘yan ta’addan da su ka halaka sojoji biyu, mace da namiji da ke shirin yin aure ya bayyana cewa yana cikin wadanda suka yi aika-aikar
  • Kamar yadda wata sautin murya ta bayyana, dan bindigan ya bayyana cewa sun yi hakan ne a matsayin ramuwar gayya akan kisan da sojoji su ke yi musu
  • An samu bayanai akan yadda sojojin su ke hanyar su ta zuwa Jihar Imo domin a yi bikin aurensu, inda ‘yan bindigan su ka halaka su a wani wuri da har yanzu ba a sani ba

Kisan gillar da aka yi wa wani soja, A. M Linus da matar da ya ke shirin aure, yayin da su ke hanyarsu da zuwa Jihar Imo ya janyo cece-kuce a kasar nan.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Bayan kisan ne wani dan bindiga wanda ya ce yana cikin wadanda su ka yi ajalinsu ya bayyana dalilinsu na tafka laifin.

Abinda Yasa Muka Fille Wa Soja Da Matarsa Kai a Hanyarsu Na Zuwa Ɗaurin Aurensu, Ɗaya Cikin Makasan Ya Magantu
Wani da ake zargin yana cikin yan bindigan da suka kashe sojoji mata da miji ya yi magana. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

An samu rahoto akan yadda su ke hanyarsu ta zuwa bikin aurensu kafin ‘yan ta’addan su tare su su kuma datse musu rayuwarsu.

Daily Trust ta ruwaito wata murya ta wayar salula da aka dauka, ta daya daga cikin ‘yan bindigan da su ka halaka sojojin yayin da ya ke yi wa wata kawar sojar bayani.

An ji muryar wani namiji yana cewa saboda hare-haren da sojojin su ke kai musu ya sanya su ka halaka sojojin a matsayin ramako.

A wannan gabar ne wacce dan bindigan ya ke yi wa bayanin ta fashe da kuka yayin da dan bindigan ya ke kwasar nishadi.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

Duk da dai kafafen labarai ba su tabbatar da muryar ba, amma yana da alaka da mummunan lamarin da ya auku kuma mutane sun nuna rashin jin dadinsu akan yadda lamarin ya faru.

Mayakan IPOB da ESN su na yawan shan caccaka, kuma ana zarginsu da addabar yankin da farmaki iri-iri. Sun dade su na kai wa jami’an tsaron yankin Kudu maso Gabas farmaki.

Idan ba a manta ba, kisan sojojin ya janyo surutai daga ‘yan Najeriya da ke amfani da kafafen sada zumunta.

MaryAnn E Eriom ta rubuta:

“Su na ta halaka nasu mutanen. Lokacin da su ka gama kashe-kashen za a ga saura mutane nawa ne za su rage don morar Biafra, sau nawa ka ke jin irin wannan yana faruwa a Gabas duk da sunan kasar Oduduwa? Ku ci gaba da lalata yankin ku. Sa’ar su ta kusa karewa ai.”

Ada Kate Uchegbu ta ce:

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Kai Wa Tawagar Kwamanda Hari a Taraba

“Asalin makiyan Ibo ne su ka halaka sojojin don su nuna daidai ne ayyukan da su ke yi a Kudu maso Gabas. Babu kungiyar Ibo da za ta halaka mutum irin wannan. Za a dauki fansar duk wani zalinci da aka yi wa Ibo watarana. Ba za ku iya hada kan Najeriya ba don kun halaka matasan Ibo.”

Hotunan Wasu Sojoji Miji Da Mata Da Aka Fille Wa Kai a Hanyarsu Ta Zuwa Imo

Tunda farko, mun rahoto muku cewa wani sojan Najeriya mai suna AM Linus tare da matarsa an kashe su a hanyarsu ta zuwa Jihar Imo a ranar Asabar.

A halin yanzu babu cikakken bayani dangane da harin a lokacin hada wannan rahoton amma Daily Trust ta tattaro cewa an kai musu harin ne domin su sojoji ne.

Wannan harin shine na baya-baya cikin hare-haren da ake kai wa jami'an tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Mutanen Gari Sun 'Tarwatse' Sun Shiga Daji Bayan Da 'Yan Bindiga Suka Kai Hari a Neja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164