Bayan wata 11, Buhari ya dawo Twitter, 'yan Najeriya sun yi masa martani

Bayan wata 11, Buhari ya dawo Twitter, 'yan Najeriya sun yi masa martani

  • A ranar 2 ga watan Maris, Shugaba Buhari ya yi wallafa a shafinsa na Twitter, karon farko tun cikin watanni 11 da suka gabata
  • A wallafar da yayi, ya saka hotunan sallah tare da yi wa 'yan Najeriya barka da sallah da kuma batun tsaro a kasar nan
  • Sai dai 'yan Najeriya sun caccake shi inda wasu suke alakanta dawowarsa Twitter bayan haramta ta da yayi da gabatowar zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma amfani da Twitter bayan kwashe tsawon watanni 11 baya amfani da kafar sada zumuntar zamani.

A watan Yunin 2021, gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da ayyukan Twitter bayan kafar sada zumuntar ta goge wata wallafar shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi kan 'yan awaren IPOB.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

Bayan wata 11, Buhari ya dawo Twitter, 'yan Najeriya sun yi masa martani
Bayan wata 11, Buhari ya dawo Twitter, 'yan Najeriya sun yi masa martani. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Bayan tattaunawa da kafar sada zumuntar na tsawon watanni, an dage haramcin amfani da ita a ranar 13 ga watan Janairu.

A jerin wallafar da shugaban kasa yayi domin shagalin idin karamar sallah a ranar Litinin, Buhari ya yi magana kan yadda yaki da ta'addancin Boko haram ya dauka lokaci amma yace ana hango nasara nan kusa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Najeriya sun yi wa Buhari martani

Daga wannan wallafar, 'yan Najeriya sun yi caa a kan shugaban kasan ganin cewa ya kwashe watanni 11 rabonsa da rubutu a kafar.

Ga wasu daga cikin martanin 'yan Najeriya:

@EditPeter, cewa yayi: "Toh shugaban kasa, daga bisani ka yanke hukuncin dawowa Twitter."
@_boom4sure cewa tayi: "Da farko na gaza yarda cewa wallafa nake gani daga shugaban kasa. Toh shugaban kasa, ka kuma dawo manhajar da ka haramta kwanakin baya? Na fahimce ka, zabe ne ya gabato."

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

@williamsefe16 ya ce: "Wai wai, wallafa ta farko tun bayan da ya haramta Twitter."

Dakatar da Twitter: Gwamnati ta ba da alamar yaushe za a dawo yin Twitter

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta bayyana dakatar da Twitter a Najeriya a matsayin na dan wani lokaci, inda ta ba da alamun cewa nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su samu samu damar sake shiga kafar ta yanar gizo.

Legit.ng ta lura cewa wannan bayanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni.

Yayin da yake karin haske kan dalilin da ya sa aka dakatar da Twitter, Shehu ya bayyana matakin gwamnatin a matsayin "na wani lokaci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel