Yan sanda sun damƙe kasurgumin shugaban masu ta'addanci a Ogun

Yan sanda sun damƙe kasurgumin shugaban masu ta'addanci a Ogun

  • Gwarazan yan sanda sun cika hannu da wani kasurgumin shugaban yan asiri da suka jima suna nema a jahar Ogun
  • Kakakin rundunar yan sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce wani bayanin sirri ne ya taimaka aka kama mutumin
  • Kwamishinan yan sandan jihar ya ba da umarnin binciko tuhume-tuhumen dake kansa don kai shi gaban Kotu

Ogun - Dakarun yan sanda sun samu nasarar cafke wani kasurgumin shugaban yan Asiri wanda ake zargin ya addabi mutanen yankunan Abeokuta da Ifo a jihar Ogun.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, kamar yadda Punch ta rahoto.

Oyeyemi ya bayyana cewa wanda ake zargin Rotimi Adebiyi, da aka fi sani da AKA Paracetamol ya jima a cikin jerin mutanen da hukumar yan sanda ke nema ruwa a jallo kan hannunsa a rikicin kungiyoyin asiri a Ogun.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Taswirar jihar Ogun.
Yan sanda sun damƙe kasurgumin shugaban masu ta'addanci a Ogun Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar kakakin yan sanda, mutumin da ake zargin shi ne shugaban ƙungiyar Asiri da ake wa laƙabi da Eiye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zakila shi ke jagorantar yan kungiyar suna shigowa cikin garin Abeokuta su aikata ta'addanci sannan su koma maɓoyar su.

A Sanarawar, kakakin yan sandan ya ce:

"Dakarun yan sanda, yayin da suke aiki kan wasu bayanan sirri suka farmaki maɓoyarsa da misalin ƙarfe 1:30 na ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu, 2022, inda suka yi nasarar cafke shi."
"Daga cikin makaman da suka samu tattare da shi akwai, ƙaramar bindigar hannu Fistol, jakar harsasai, layu, Adda da kuma haramtattun kwayoyi."

Wane mataki yan sanda zasu ɗauka nan gaba?

Oyeyemi ya ce kwamishinan yan sanda na jihar Ogun, Lanre Bankole, ya ba da umarnin tsananta bincike kan dukkn ayyukan da ake zargin sa domin samun hujja a kansa a gabatar da shi a Kotu.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

A wani labarin na daban kuma Gwamna a Najeriya ya ƙara mafi karancin Albashi daga N30,000 zuwa N40,000

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙara mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa daga N30,000 da gwamnatin tarayya ta ƙayyade zuwa N40,000.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana wannan ƙarin ne yayin taya ma'aikata murnar 'Ranar ma'aikata ta duniya' ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262