'Yar takara mai shekara 102: EFCC, ICPC su kama duk dan takarar da ya siya fom N100m

'Yar takara mai shekara 102: EFCC, ICPC su kama duk dan takarar da ya siya fom N100m

  • An bukaci hukumomin yaki da rashawa da su yi ram da duk wani 'dan siyasa ko kungiyar da ta siya fom din takara kan kudi har N100 miliyan
  • Babbar alkaliya Josephine Ezeanyaeche ce tayi kiran ga EFCC, kungiyoyi masu zaman kansu na yaki da lamurran da suka shafi rashawa da sauransu
  • Sai dai tsohuwa mai shekaru 102 dake takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023 ta lashi takobin kawo canji tunda matasa masu jini a jika na kasa sun gaza

An tura sako ga hukumar yaki da rashawa, EFCC da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC da su yi ram da duk dan takarar da ya siya fom kan kudi N100 miliyan.

Tsohuwa mai shekaru 102, 'yar takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023, Mrs Josephine Ezeanyaeche ce ta tura sakon.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

'Yar takara mai shekara 102: EFCC, ICPC su kama duk dan takarar da ya siya fom N100m
'Yar takara mai shekara 102: EFCC, ICPC su kama duk dan takarar da ya siya fom N100m. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Kai tsaye, tana bukatar jami'an tsaro su damko gami da gurfanar da duk wani 'dan siyasa ko kungiyar da ta siya fom din takara N100 miliyan na duk wata jam'iyyar siyasa.

A cewarta, in dai da gaske hukumomin yaki da cin hanci da rashawa zaman kansu suke, kuma suna aiki yadda ya dace, bai kamata a tunatar da su cewa babu wani 'dan siyasa da zai amayo irin wannan kudin ba tare da ya saci dukiyar al'umma ba, jaridar Punch ta ruwaito.

Josephine Ezeanyaeche ta bukaci EFCC da ICPC da su yi ram da 'yan siyasan da suka siya fom din takara N100 miliyan.

Ta fadi hakan ne a lokacin da ta gabatar da fom din takarar jam'iyyar ta na jam'iyyar AAC ga mutanen ta a Igboukwu cikin karamar hukumar Aguata na jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Haka zalika, ta cigaba da kira ga INEC da sauran hukumomin da suka shafi haka da su samar da dokar da za ta daidaita yawan kudin da ake kashewa wajen siyan fom din takara da gudanar da zabe a matsayin wani bangaren rage cin hanci da rashawa.

Ta kara da cewa, dalilin da yasa ta zabi takara kujerar shugaban a shekarar 2023, shinne don kawo canji mai dorewa tunda matasa masu jini a jika sun gaza.

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

A wani labari na daban, dattijuwa Iyom Josephine Ezeanyaeche, mai shekaru 102, wacce aka fi sani da Living Legend ko Mama Africa, ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Misis Ezeanyaeche wadda ‘yar asalin karamar hukumar Agwata ce a jihar Anambra ta bayyana aniyar ta ne a lokacin da ake hira da ita a gidan talabijin na NTA tare da mambobin kungiyar Voice for Senior Citizens of Nigeria, wata kungiyar jin kai da ta kafa.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng