Yanzu-yanzu: Ba'a ga watan Shawwal ba a Saudiyya, za'a cika 30

Yanzu-yanzu: Ba'a ga watan Shawwal ba a Saudiyya, za'a cika 30

  • Bayan faduwar rana, hukumomi a kasar Saudiya ta yi sanarwa game da lamarin ganin watar Shawwal
  • Misalin karfe 6:30 agogon Saudiyya, ba'a ga jinjirin wata ba
  • Musulmai a fadin kasa mai tsarkin zasu karashe azuminsu na Ramadan ranar Lahadi

Labari da duminsa dake shigowa na nuna cewa ba'a ga jinjirin watan Shawwal a kasar Saudiyya ba a yau Asabar, 29 ga watan Ramadan, wanda yayi daidai da 30 ga watan Afrilu.

Shafin Masallacin Makkah da Madina a jawabin da ya saki yace ranar Litnin hukumomi a kasar Saudiyya suka sanar za'a Sallar idin bana.

Jawabin yace:

"Ba'a ga jinjirin watan Shawwal 1443 ba yau, sakamakon haka: Ranar Litinin, 2 ga watan Mayu, 2022 za'a yi Eid Al Fitr."
"Watar Ramadan 1443 za ta cika talatin."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar

Watan Ramadan zai cika kwana 30 a Nigeria da Kasar Saudi Arabia

Wani masani, Adamu Ya'u ya yi bayanin cewa watan Ramadan zai cika Kwana 30 a Nigeria da Kasar Saudi Arabia

A bayanan da marubuci kuma masanin ilmin sararin samaniya yayi, ya ce Za'a Samu kisfewar Wata, a cikin Watan Shawwal.

Yace:

Na Tabbata Saudi_Arabia Ba za su ga Wata a ranar Duban Fari ba, kuma babu wanda zai yi musu Tawaye.
Amma mu a Nigeria kusan Abinda ya faru a wanchan shekarar ina tunanin zai sake faruwa, kamar yadda wanchan shekarar muka tabbatar Babu Wata a Sama Bayan Faduwar Rana a ranar Duban Fari, amma a haka aka samu wasu wai Sun ga Wata.
Kuma wasu da basu san meye ilimi akan wata ba suna ta sukar Mai Alfarma Sarkin Musulmi akan wai anga wata yaki tabbatar wa, Daman ai ba zai amince ba, saboda yanzu ilimi yazo ba yadda za'a yi amfani da cewa anga wata Alhali babu wata a ranar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng