Dausayin Ramadan: Abubuwa 10 da basu da amfani, Sheikh Aminu Daurawa

Dausayin Ramadan: Abubuwa 10 da basu da amfani, Sheikh Aminu Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malam ya yi bayani kan jerin abubuwa 10 da basu da amfani ga Musulmi.

1. Amfanin ilimi aiki da shi, Ilmin da ba a yi aiki da shi ba, bashi da amfani ga mai shi,

اللهم اني اعوذ بك من علم لا ينفع

2. Aikin da babu iklasi da bin Sunnah a cikin sa. bashi da amfani.

من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Dukiyar da ba a ciyar da ita ba, kuma wanda ya tara bai amfana da ita ba a duniya da lahira. ita ma ba ta da amfani.

Kara karanta wannan

2023: Jerin ‘Yan shekara 20 Zuwa 30 da suka Shiga Takarar Majalisar Tarayya

وابتغ فيما أتاك الله الدار الآخرة ولا تنس تصيبك من الدنيا

4. Zuciyar da babu kaunar Allah a cikin ta da shuƙin gamuwa da shi da jin daɗin ambaton sa.

. من أحب لقاء الله، احب الله لقاءه

5. Jikin da ba a sarrafa shi wajan biyayya ga Allah.

فاعني على نفسك بكثرة السجود.

6. Soyayyar da babu ɗa'a da hidma ga masoyi a cikin ta. da yi masa biyayya.

من أحب لله، وكره لله، وأعطى لله، ومنع لله، فقد استكمل الإيمان.

7. Lokacin da ya tafi a banza ba a ci moriyar sa ba wajan gyara kuskure da kuma aikin mai kyau don gobe ƙiyama.

نعمتان مغبون فيهما كثير من الناس، الصحة والفراغ.

8. Tunani mara amfani, cikin abin da zai amfani mutum ko a duniya ko a lahira.

كن في الدنيا كانك غريب او عابر سبيل.

9. Yin Hidma ga wanda yi masa hidmar ba za ta tsinana maka komai ba a duniya ko a lahira.

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Fallasa Wasu Yan Takara, Ya Gargaɗi 'Yan Najeriya Kada Su Zaɓe Su a 2023

تعس عبد الدينار والدرهم.

10. Ka zama mai kwaɗayin abin hannun wani ko ka zama mai tsoro ga wani mahaluƙi wanda ba shi da wani tasiri wajan tsinana maka komai a rayuwar ka. Shi ma ta kansa zai yi ranar Alƙiyama, sai wanda Allah ya yarda da shi ya kuma bashi izni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel