An Gurfanar Da Matar Aure, Adama, Gaban Kotu Bisa Zarginta Da Kiran Makwabciyarta Mayya

An Gurfanar Da Matar Aure, Adama, Gaban Kotu Bisa Zarginta Da Kiran Makwabciyarta Mayya

  • An gurfanar da wata matar aure, Adama Bello, mai shekaru 20 a ranar Alhamis a gaban wata babbar kotun Gwagwala da ke Abuja, bisa zarginta da kiran makwabciyarta da mayya
  • ‘Yan sanda suna tuhumar Bello, wacce ke zama a Yangoji da ke karamar hukumar Kwali da bacin suna kamar yadda lauyan mai kara, Abdullahi Tanko ya shaida wa kotu
  • Ya kuma bayyana wa kotu sautin muryar wacce ake zargin wanda ta ke kiran makwabciyartata da mayya tana zarginta da yunkurin halaka ta

Abuja - Adama Bello, matar aure mai shekaru 20 ta gurfana gaban wata babbar kotu da ke Gwagwalada a Abuja ranar Alhamis inda ake zarginta da kiran makwabciyarta da mayya, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo

Bello, mazauniyar Yangoji da ke karamar hukumar Kwali tana fuskantar tuhuma a gaban hukuma na bata wa makwabciyarta suna.

An Gurfanar Da Matar Aure Gaban Kotu Bisa Zarginta Da Kiran Makwabciyarta da Mayya
An Gurfanar Da Matar Aure Gaban Kotu Bisa Zarginta Da Kiran Makwabciyarta Mayya. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Abdullahi Tanko, lauyan mai kara ya sanar da kotu cewa a ranar 6 ga watan Afirilu cewa Zainab Samaila ta gabatar wa ‘yan sanda kara, rahoton The World News ta rahoto.

Har kyauta wacce ke kara ta bai wa wacce ta ke kara daga baya kuma zargi ya biyo baya

A cewar Tanko, mai karar ta je sunan jaririn wacce ta ke kara har tana kai mata kyautar kwalba daya na man gyada da N200.

A cewarta, kamar yadda The Nation ta nuna, bayan ta amshi kyautukan ne ta koma tana zarginta tare da bata mata suna.

Ya ce wacce ake karar ta zargi mai karar da zama mayya inda ta ce ta yi yunkurin halaka ta.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro a kasar Saudi Arabia sun damke mabarata a Masjid Al-Haram

A cewar Tanko, yanzu haka akwai sautin muryar da mai karar ta gabatar wa ofishin ‘yan sanda yayin da ake bincike.

Lauyan ya ce laifin ya ci karo da sashi na 391 na Penal Code.

Sai dai wacce ake kara ta ki amsa laifukan da ake zarginta da su.

Alkali ya shimfida sharuddan beli ga wacce ake kara

Alkalin, Sani Umar ya bayar da belin wacce ake kara a N200,000, sannan ya bukaci ta gabatar da tsayayye daya.

Umar ya ce wajibi ne tsayayyen wanda ake karar ya kasance mazaunin kusa da kotun sannan ya gabatar wa kotu hotunansa guda biyu wadanda bai dade da daukarsu ba.

A cewarsa, har ila yau, wajibi ne tsayayyen ya gabatar da hoton katin shaidarsa da kuma adireshin gidan da ya ke zama ga kotu.

Ya ce in har wacce ake karar ta gaza cike sharuddan kotu, za a garkameta a gidan gyaran halin Najeriya da ke Suleja.

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Yuni.

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164