Karamar Sallah: A fara duban wata daga ranar Asabar, inji hukumomin kasar Saudiyya
- Gwamnatin kasar Saudiyya ta bayyana bukatar a fara duban jinjirin watan Shawwal daga ranar Asabar mai zuwa
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da musulman duniya ke ci gaba da azumtar watan Ramadana mai alfarma
- Hukumar ta kuma bayyana cewa, mazauna kasar na iya ba da bayanai ga hukumomi kan samun labarin ganin watan
Riyadh, Saudiyya - Kotun kolin Saudiyya a ranar Alhamis ta umurci masu sa ido da su nemi jinjirin watan Shawwal na shekarar Hijira 1443 da yammacin ranar Asabar 29 ga watan Ramadan wanda zai zo daidai da 30 ga Afrilu, 2022.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya nakalto daga kotun na masarautar Saudiyya cewa, an yi kira ga 'yan kasar da mazauna yankin da su nemi jinjirin watan tare da kai rahoton duk wani abin da suka gani ga hukumomin da ke kusa dasu.
Haka kuma ganin jinjirin watan na Shawwal zai kasance ranar karamar sallah da ka iya zuwa ko dai a ranakun Lahadi ko kuma Litinin din mako mai zuwa, inji shafin yanar gizon masallatai masu alfarma na Haramaini.
Hakazalika, ministan kula da harkokin addinin musulunci, karkashin jagorancin Sheikh Dr. Abdullatif Bin Abdulaziz Al-Sheikh ya umarci rassan ma'aikatar da su shirya dukkan masallatai da wuraren ibada domin karbar masallata a sallar Idi, inji rahoton Daily Nigerian.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masana ilmin taurari da dama sun ce akwai karancin tsammanin ganin jinjirin watan a ranar Asabar da yamma kuma watan Ramadan na 1443 zai iya cika kwanaki 30, kamar yadda rahotanni a baya suka bayyana.
Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030
A wani labarin, jaridar Arab News ta tattaro cewa, musulmai za su yi azumin Ramadana sau biyu a shekara ta 2030, kamar yadda wasu masana ilmin taurari suka yi hasashen.
Masana sun ce watan azumi zai shigo sau biyu a wannan shekara ta 2030, na farko a watan Janairu, sannan kuma a karshen watan Disamba, lamarin da ya taba faruwa a shekarar 1997.
Dalilin da ke tattare da haka ya ta’allaka ne da bambamcin da ke akwai tsakanin Kalandar Hijira, wanda ya ginu a kan zagayowar wata, da kalandar Miladiya da ke tafiya da zagayawar duniya a gefen rana.
Asali: Legit.ng