Daren Lailatul Kadri: Aisha Buhari ta yiwa mutanen Zamfara addu’a ta musamman

Daren Lailatul Kadri: Aisha Buhari ta yiwa mutanen Zamfara addu’a ta musamman

  • Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta roki Allah a kan ya fitar da mutanen jihar Zamfara daga mawuyacin hali da suke ciki
  • Aisha ta yi rokon ne cikin kan-kan da kai tare da yin tawassali da daren Lailatul Kadari wanda ke fadawa a goman karshe na Ramadana
  • Jihar Zamfara dai na fama da matsalar ta'addanci da suka hada da kashe-kashe da kuma sace-sacen mutane

Abuja - Yayin da Musulmi ke cikin goman karshe na watan Ramadan, ana sanya ran dacewa da daren Lailatul Kadari a cikin dararen.

Allah ya fifita wannan dare na Lailatul Kadari sannan ya ba shi wata daraja da ɗaukaka ta musamman, kuma ya keɓance shi da wata falala ta musamman wadda bai bawa sauran darare ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

Daren Lailatul Kadri: Aisha Buhari ta saka mutanen Zamfara a addu’a
Daren Lailatul Kadri: Aisha Buhari ta saka mutanen Zamfara a addu’a Hoto: SolaceBase
Asali: Depositphotos

Hakan ce ta sanya uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha, ta yi amfani da wannan dama wajen yiwa al’ummar jihar Zamfara addu’an fita daga mawuyacin hali da suka riski kansu a ciki.

A cikin wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram, Aisha Buhari ta roki Allah da ya fitar da mutanen Zamfara da na kasar daga yanayin albarkacin daren na Lailatul Kadari.

Ta rubuta a shafin nata:

“Allah ya fitar da mu da mutanen jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Kadri, Ameen!”

Yankin arewa maso yammacin kasar musamman jihar Zamfara dai na fama da matsalar tsaro da suka hada da fashi da makami da sace-sacen mutane.

Lamarin na kara gaba ne a kullun kwanan duniya, har ta kai ana zargin wasu sarakunan gargajiya da taimaka wa ayyukan ta’addanci a jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga

A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta tsige wasu sarakuna biyu da hakimi daya bisa zargin taimaka wa ayyukan ta'addancin ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar jihar.

Ibrahim Dosara, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Zamfara ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron Majalisar Zartaswar Jihar a Gusau, babban birnin Jihar.

Wadanda hukuncin gwamnatin ya shafa sun hada da Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da kuma Sulaiman Ibrahim wanda ya taba zama Hakimin Birnin Tsaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel