NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol na 2.3m, 396Kg na Codeine a Kaduna

NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol na 2.3m, 396Kg na Codeine a Kaduna

  • Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi ta jihar Kaduna ta bayyana yadda ta kama kwayoyin tramadol na 2.3 miliyan masu nauyin 1.2 tonnes a Zaria
  • Haka zalika, kakakin hukumar ya bayyana yadda aka sake kama maganin tari na codeine mai nauyin 396kg a bayan wata Toyota bus cikin buhunhuna 15 karkashin kwalaye
  • A cewar hukumar, kwalaben maganin tari na codeine guda 2,919 sun kai darajar N10.5 miliyan, inda suka cigaba da bayyana yadda hukumar ta kama masu safarar kwayoyi 73 a watan Afirilu

Kaduna - Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi ta jihar Kaduna (NDLEA) ta ce jami'anta sun kama kwayoyin tramadol na 2.3 miliyan a cikin jihar.

Mai Jama'a Abdullahi, kakakin rundunar NDLEA ta Kaduna, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol na 2.3m, 396Kg na Codeine a Kaduna
NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol na 2.3m, 396Kg na Codeine a Kaduna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewar Abdullah, kwayoyin sun kai nauyin 1.2 tonnes, sannan an kama maganin tari na codeine yayin da jami'an hukumar suka kai wani samame a ranar Litinin da Talata.

Kakakin rundunar ya cigaba da bayyana yadda aka kwace kwayoyin tramadol din a karamar hukumar Zaria a ranar Litinin, yayin da aka yi ram da wanda ake zargin a wata gonar kaji dake jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da labarta yadda jami'an hukumar yayin sintiri suka tsaya, gami da bincikar mota kirar Toyota bus, mai lamba RBC 752 XE inda suka ga buhunhunan maganin tari na Codeine guda 15.

"An boye buhunhunan maganin tarin codeine din karkashin kwalayen giya da na lemun malt," a cewarsa.
"Direban ya bayyanawa jami'an hukumar yadda aka lodo miyagun kwayoyi daga kasuwar Onisha dake Anambra zuwa Kaduna.
"Kwalaben maganin tari na codeine 2,919 masu nauyin 395kg, sun kai darajar N10.5 miliyan."

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta garkame dukiyoyin Abba Kyari dake Maiduguri, gidaje 6, Plaza mai shaguna 100

Haka zalika, ya ce ana cigaba da bincike don gano wanda aka yi kokarin kai wa sakon a Kaduna.

Daga karshe, Abdullahi ya ce a cikin watan Afirilu ne aka kama mutane 73 a fadin jihar, wadanda ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi.

Abuja: NDLEA ta kama hodar iblis da aka yi mata basaja a jakunkunan ganyen shayi

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana yadda tayi ram da wani Pascal Okolo bayan ta kama shi dumu-dumu da hodar iblis.

A wata takarda da kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a shafinsu na Twitter, ya bayyana yadda aka boye hodar iblis mai nauyin 4.1 kg a jakunkunan shayi.

Ya ce, an ga hakan ne yayin bincikar kayansa na jirgin saman da ya iso Najeriya daga Sao Paulo ta Doha a 17 ga watan Afirilu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng