Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

  • Daga karshe, majalisar dattawa ta amince a haramtawa yan Najerya biyan masu garkuwa kudin fansa
  • Shugaban majalisar dattawa yace doka za ta iya taimakawa wajen magance matsalar tsaron kasa da kuma inganta tattalin arziki
  • Daga bisa an turawa majalisar wakilan tarayya don ta amince kafin a aikawa shugaban kasa ya rattafa hannu

Abuja - Majalisar dattawan tarayya ta yiwa dokar ta'addanci ta 2013 gyaran fuska domin haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa idan suka bukata hannun iyalan wadanda suka sace.

Majalisar bayan kyakkyawan dubin da kwamitin harkokin doka tayi kan lamarin, ta amince da gyaran fuskar kuma yanzu Shugaba Buhari za'a kaiwa ya rattafa hannu.

Shugaban kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti Central), ne ya gabatar da rahoton.

A jawabinsa, ya bayyana cewa babbar manufar dokar itace dakatad da garkuwa da mutane don kudi tunda abin ya zama ruwan dare.

Kara karanta wannan

Malama ta tafka hatsari, ta rasu tana hanyar kai wa dalibanta kyautukan ba-zata

A cewarsa:

"Samar da dokokin don yakin da hanyoyin samun kudin yan ta'adda ko shakka babu zai taimaka wajen rage cinikayyar bayan fagge cikin al'ummarmu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kafa wannan doka zai kare Najeriya daga sanyata cikin jerin kasashen da hukumar Financial Action Task Force (FATF) ta duniya ta sanyawa ido da kuma wasu illoli wanda ya hada da sanyawa Najeriya wasu takunkumi na kudi da zai shafi mutuncin kasar."

Majalisar dattawa
Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa Hoto: @NGRSenate
Asali: UGC

Shi kuwa Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa wannan doka za ta taimaka wajen karfafa yaki da matsalar tsaro da gwamnatin tarayya ke yi.

Yace wannan doka za ta iya magance matsalar tsaron kasa da kuma inganta tattalin arziki.

Yace:

"Bari in fayyace bayani, yakin rashin tsaro, garkuwa da mutane, ta'addanci da sauran su ba hakkin gwamnati bane kadai."
"Ya kamata al'ummar Najeriya su bada nasu goyon bayan saboda jami'an tsaro na bukatar bayanai."

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

Yanzu an turawa majalisar wakilan tarayya don ta amince kafin a aikawa shugaban kasa ya rattafa hannu.

Harin jirgin kasan Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun saki hotunan mutane 62 da suka sace

Wata guda cir bayan harin da yan bindiga suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna inda akalla mutum 9 suka hallaka, yan ta'addan sun saki hotunan fasinjojin dake hannunsu.

Wata Lakcara a jami'ar jihar Kaduna, Bilkisu Yero, ce ta saki hotunan a shafinta na Facebook.

Hotunan da aka saki ranar Litinin ne karo na uku yan bindigan zasu saki bidiyo ko hoto dake nuna cewa wadanda suka sace na raya cikin lafiya.

Har yanzu, gwamnatin Najeriya ta gaza fadin takamammen adadin mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng