Harin jirgin kasan Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun saki hotunan mutane 62 da suka sace
- Yan bindiga sun saki hotunan mutane 62 da suka sace a Harin jirgin kasan Abuja-Kaduna a watan Maris
- Cikin hotuna ukun akwai mata ashirin da uku (23) da kuma maza talatin da tara (39) zaune kan leda
- Da alamun yan bindigan na bibiyan kafafen yada labarai saboda wannan karon sun rufe bayansu
Wata guda cir bayan harin da yan bindiga suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna inda akalla mutum 9 suka hallaka, yan ta'addan sun saki hotunan fasinjojin dake hannunsu.
Wata Lakcara a jami'ar jihar Kaduna, Bilkisu Yero, ce ta saki hotunan a shafinta na Facebook.
Hotunan da aka saki ranar Litinin ne karo na uku yan bindigan zasu saki bidiyo ko hoto dake nuna cewa wadanda suka sace na raya cikin lafiya.
Har yanzu, gwamnatin Najeriya ta gaza fadin takamammen adadin mutanen da aka sace.
Wata daya kenan suna rike da fasinjojin kuma mutum daya kadai, Alwan Hassan, suka saki bayan ya biya kudi N100m.
Mutanen dake cikin hotunan:
A cikin daya daga cikin hotunan, akwai mutum 23, yawanci mata da yara 3.
Yan bindigan sun shimfida leda a kasa yayinda suka rufe bayansu da zanin gado.
A cikin hoto na biyu kuwa, akwai maza 17 zaune cikin sahu.
A hoto na uku, akwai maza 16.
Legit ta samu ji daga bakin wani mazaunin Zaria, Muhammad Malumfashi, cewa daya daga cikin wadanda ke cikin hotunan sunansa Sadiq Ango Abdullahi, dan siyasa ne kuma mai niyyar takaran kujerar dan majalisar wakilai.
Wani ma'aikacin gwamnati, Yusuf Atta,a Facebook yace:
"Wayyo yar uwata da mahaifiyata. Sune na farko da ta biyu daga dama zaune a kasa. Allah ya fiDda ku baki daya."
Habiba AbdulAziz kuwa tace:
"Wayyo Allah, ga mahaifiyata da yar uwata. Allah ya fiddasu daga wajen wadannan mutanen."
Wani Isma'el Yarima kuwa yace:
"Ga yar uwata caN. Allah ya kare ku."
Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa binciken farko-farko da ta gudanar kan harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya nuna cewa an fara samun hadin kai tsakanin yan bindiga da yan Boko Haram.
Daily Trust ta rahoto cewa Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswar da shugaba Buhari ya jagoranta ranar Laraba.
Asali: Legit.ng