Kano: Ƴan Hisbah Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Masu Ƙwacen Waya Ne a Masallaci a Cikin Watan Ramadana

Kano: Ƴan Hisbah Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Masu Ƙwacen Waya Ne a Masallaci a Cikin Watan Ramadana

  • Yan Hisbah sun kama wasu matasa maza da mata su takwas da ake zarginsu da satar waya da wasu laifukan a masallacin Al-Furqan, GRA, Nasarawa
  • Babban Kwamandan Hisbah na Kano, Dr Muhammad Sani Ibn Sina ya tabbatarwa manema labarai kamen a Kano
  • Sheikh Ibn Sina ya yi kira ga al'umman gari su rika saka idanu sosai, su kuma kai rahoton duk wani ko wata da suke zargin yana aikata laifin

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce kama matasa maza da mata su takwas da ake zargin masu kwacen waya ne da wasu miyagun ayyuka a masallacin Al-Furqan da ke Nasarawa GRA.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa Babban Kwamandan Hisbah, Dr Muhammad Sani Ibn Sina ya tabbatarwa manema labarai kamen a Kano.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Kano: Ƴan Hisbah Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Masu Ƙwacen Waya Ne a Masallaci a Cikin Watan Ramadana
Yan Hisbah a cikin motarsu yayin sintiri a Kano. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin su takwas da rana kuma suna shaye-shayen miyagun kwayoyi da wasu abubuwan a filin tseren dawakai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma, ya bayyana abin da suke aikatawa bai dace ba domin musulunci ya hana musulmi aikata badala musamman a lokacin azumin watan Ramadana, rahoton Nigerian Tribune.

Sheikh Ibn Sina ya yi kira ga al'umman gari su rika saka idanu sosai, su kuma kawo rahoton duk wani da suke zargin yana aikata laifi da hukumomin da suka dace.

Ya ce hukumar Hisbah ta Jihar Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kawar da dukkan miyagun ayyuka a jihar.

Ya kara da cewa tuni an mika wadanda ake zargin zuwa ga hukumomin da suka dace domin a dauki mataki na gaba a kansu.

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

Kara karanta wannan

Karin kudi 100%: Maniyyata aiki Hajji sun fusata, sun fito zanga-zanga, sun fadi bukatarsu

A wani rahoton, Hukumar Hisbah reshen jihar ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda

The Nation ta ruwaito. Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Kuma an kama su ne bayan kai samamen da hukumar ta yi a gidajen giya, gidajen karuwai da sauran wuraren da mutanen banza ke zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164