Hotuna: Yadda sojojin Najeriya suka ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
- Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar ragargazar wasu 'yan ta'addan Boko Haram a wani yankin jihar Borno
- Hakazalika, rundunar ta ce dakarunta sun kwato wasu kayayyaki daga hannun 'yan ta'addan a yayin samamen
- Hotunan da muka samo sun nuna yadda gawarwakin 'yan ta'addan ke watse a kasa bayan kammala aikin na soji
Borno - Rundunar sojin Najeriya ta fitar da wasu hotunan da ke nuna yadda ta lalata mafakar 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a yankin Kasha Kasha ta jihar Borno a yau Talata, 26 ga watan Afrilu.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rundunar ke kara kaimi wajen dakile munanan ayyukan 'yan ta'adda a Arewancin Najeriya.
Rundunar ta ce, dakarun bataliya ta 195 tare da mambobin CTJTd ne suka yi wannan aiki a wani samamen da suka kai kan 'yan ta'addan.
Hotunan da Legit.ng Hausa ta samo daga shafin Twitter na Rundunar Sojin Najeriya sun nuna alamar gawargwakin 'yan ta'addan da kuma kayayyakin da aka lalata.
Hakazalika, sanarwar d ake tattare da hotunan ta bayyana cewa, an kwato kayayyakin barna daga hannun 'yan ta'addan.
Sanarwar ta ce:
"Jaruman dakarun bataliya ta 195 tare da mambobin CJTF a wani samame da suka kai sun ragargaji kungiyar ISWAP/BokoHaram a Kasha Kasha a jihar Borno a yau 26 ga Afrilu 2022. An kuma kwato makamai da alburusai da dai sauransu."
Kalli hotunan:
Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba
A wani labarin, rundunar sojin saman Najeriya ta lalata maboyar gungun ‘yan bindiga da dama a kewayen kauyen Kambari da ke karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m
Jiragen saman NAF sun yi ruwan bama-bamai a yankunan inda suka kashe ‘yan bindiga da dama a wani samame da suka fara kwanaki uku da suka gabata.
A farmakin akwai dakarun kasa da suka kama ‘yan bindiga da dama da 'yan leken asirinsu a kewayen Gassol da Karim Lamido duk dai a jihar.
Asali: Legit.ng