Jami'an yan sandan MOPOL sun yiwa Kwamandan Sibil Defens lilis, sun kashe dogarinsa

Jami'an yan sandan MOPOL sun yiwa Kwamandan Sibil Defens lilis, sun kashe dogarinsa

  • An zargi Jami'an hukumar Mobile Police da kai jami'an Civil Defense hari har ofishinsu a Owerri
  • Ana fargaban an yi rashin rai guda kuma mutane da dama sun samu raunuka daban-daban
  • Wasu jami'an NSCDC a jawabansu sun ce wani dan sanda ya nemi tsokanarsu kuma suka garkameshi

Rikici ya barke tsakanin yan sanda da jami'an NSCDC watau Sibil defense sakamakon rashin jituwan da ya wakana tsakanin jami'an hukumomin tsaron biyu a jihar Imo.

Leadership ta ruwaito cewa yan sandan sun kai farmaki hedkwatar NSCDC dake Owerri, ranar Litinin kuma suka yiwa kwamandansu zindir kuma suka kashe dogarinsa.

Rahoton ya kara da cewa rikicin ya fara lokacin da wani dan sanda sanye da kayan gida ya tare hanya, ya hana kwamandan NSCDC wucewa yayinda yake hanyar komawa Owerri daga Abacheke, inda matatar man sata tayi gobara.

Kara karanta wannan

Group Admin ya yi 'batan dabo da N1.8m da mambobi suka hada a WhatsApp

Jami'an yan sandan MOPOL sun yiwa Kwamandan Sibil Defens lilis, sun kashe dogarinsa
Jami'an yan sandan MOPOL sun yiwa Kwamandan Sibil Defens lilis, sun kashe dogarinsa Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Wani jami'an Sibil Defence mai suna Ikechukwu yace:

"Lokacin da dogaran kwamanda suka cewa dan sanda ya tashi daga hanya, ya ki. Sai ya kira sauran abokansa yan sanda daga hedkwatar yan sanda kuma ya bisu ofishinsu.
"Yayinda suka kai ofishin NSCDC, dan sandan ya sake tare hanya ya fito da bindigarsa yana ikirarin cewa shi dan sanda ne. Kawai sai jami'an NSCDC suka zagayeshi suka kwace bindigar kuma suka garkame shi."

Wani jami'in hukumar wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace,

"Bayan an sakeshi, sai ya dawo da rundunar MOPOL kuma suka shiga dukan jamianmu suka lalata kayan ofishinmu."

Yayinda aka fara harbe-harben bindiga, sa ya kwamandan ya fito sulhunta lamarin, amma yan sandan suka yi masa lilis kuma suka cire masa riga sukayi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Za Ta Siyo Jiragen Sama Don Yaƙi Da Wutar Daji, Ministan Harkokin Gida, Aregbesola

Har yanzu bangarorin biyu basu yi magana kan lamarin a hukumance ba.

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Shugaba Buhari ya fusata, ya ba jami'an tsaro umarnin kara kaimi wajen kawo karshen haramtattun ayyuka daga haramtattun matatan man fetur da ke aiki ba bisa ka'ida ba a yankunan kasar nan.

Hakazalika, shugaban ya bayyana kaduwarsa da jin labarin mutuwar mutane sama da 100 sakamakon irin wannan lamari a jihar Imo.

Fusatar Buhari na zuwa ne bayan wani rahoton mutuwar sama da mutane 100 ne a daren Juma’a bayan da wata matatar man fetur ta fashe a dajin Abaezi da ke karamar hukumar Ohaji-Egbema a jihar Imo ta Kudu maso Gabashin Najeriya ya karade kafafen yada labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: