Yau Talata APC za ta fara sayar da Fam na takarar zaben 2023
- Bayan matsalar da aka samu makon da ya gabata, yau za'a fara sayar da Fom din takara karkashin APC
- Fiye da abokiyar hamayyarta sau ninki biyu da rabi, APC ta ce N100m za ta sayar da Fam din takarar kujerar shugaban kasa
- Za'a gudanar zaben fidda gwanin kujeran shugaban kasa mako guda bayan gudanar da na gwamnoni
FCT Abuja - Gabanin zabukan fidda gwamnin jam'iyyar All Progressives Congress’ (APC), za'a fara sayar da Fam ga masu niyyar takara yau Talata a fadin tarayya.
An dage sayar da Fam daga karshen makon da ya gabata zuwa Yau bisa wasu dalilai.
Za'a sayar da Fam din yan takarar kujerun yan majalisar jiha a sakatariyar APC na jihohinsu, rahoton TheNation.
Hakazalika an umurci Sakatarorin tsare-tsare na jihohi 36 su karbi takardun idan aka kammala cikawa.
Amma Fom din yan majalisar dokokin tarayya, gwamnoni da shugaban kasa, hedkwatar uwar jam'iyyar dake Abuja ce zata sayar.
Kakakin jamiyyar APC,, Felix Morka, ya bayyanawa manema labarai ranar Litinin cewa yau Talata zasu fara sayarwa.
Yace:
"Mun shirya fara sayar da Fam gobe (Talata). Zamu saki bayanin tsarin yadda za'a sayar a shafinmu. Amma za'a sayar da na majalisun jiha a jihohinsu, sauran kuma a hedkwatar tarayya."
N100m muke sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yanke shawara kan farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar kujerar shugaban kasa a 2023 karkashin lemarta.
Ga jerin farashin nan:
1. Majalisar jiha- N2,000,000
2. Majalisar wakilai - N10,000,000
3. Majalisar dattawa - N20,000,000
4. Gwamna - N50,000,000
4. Shugaban kasa - N100,000,000
Asali: Legit.ng