Labari Da Ɗuminsa: Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kuɗi Dalla Biliyan 44

Labari Da Ɗuminsa: Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kuɗi Dalla Biliyan 44

  • Shugabannin gudanarwan kamfanin Twitter sun amince da tayin da Elon Musk ya yi na siyan kamfanin dandalin sada zumuntar
  • Sanarwar za ta bawa attajirin mafi arziki a duniya damar kara Twitter cikin kamfanonin da ya mallaka a yayin da ya ke kokarin kawo canji
  • Shugabannin gudanarwan na Twitter da farko ba su so amincewa da tayin ba amma daga bisani suka sauya ra'ayinsu duba da riba da ya bada

Kamfanin Twitter, a ranar Litinin ta tabbatar da cewa za ta sayarwa attajirin duniya Elon Musk kan kudi Dallar Amurka Biliyan 44, The Punch ta rahoto.

Sayar da kamfanin abin mamaki ne duba da cewa da farko mambobin kwamitin kamfanin sun ki amincewa Musk ya siya kamfanin dandalin sadarwar.

Labari Da Duminsa: Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kudi Dalla Biliyan 44
Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kudi Dalla Biliyan 44. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne kimanin mako guda bayan Musk ya sanar da niyarsa na siyan dandalin sada zumuntar da ya fi kauna kan $54.20 kowanne hannun jari.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi Sallar Jana'izar Alaafin Oba Lamidi Adeyemi

Bayan sanarwar amince masa siyan kamfanin, hannun jarin Twitter ya tashi da fiye da kashi 5 cikin 100 a ranar Litinin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Reuters ta rahoto cewa Musk ya gana da masu hannun jari a karshen mako don tattaunawa kan tayin da ya yi na siyan kowanne hannun jari kan $54.20.

A cewar rahoton, tayin da Musk ya yi na siyan kamfanin kan kudi Dalla Biliyan 43 ya sa shugabannin gudanarwar suka sauya shawararsu ta farko.

"Bawa kowa ikon bayyana ra'ayina shine ginshikin demokradiyya mai aiki, kuma Twitter dandali ce inda ake tattauna batutuwa da za su al'umma a nan gaba," a cewar Musk cikin wata sanarwa.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164