Nasara: NDLEA ta kama attajirin da ya kulla harkallar kwaya da Abba Kyari ta N3bn
- Ta fara karewa Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin harkallar kwaya da DCP Abba Kyari
- Bincike daga NDLEA ya nuna cewa an kama Ukatu ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja a sashen MM2 ta tashar jirgin saman Legas
- Wanda ake zargin ya mallaki kamfanonin harhada magunguna, kuma ana kyautata zaton yana da hannu a harkallar N3bn
Jihar Legas - Hukumar NDLEA ta samu nasarar kame Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wani attajirin da ake zargin yana da hannu a harkallar safarar miyagun kwayoyi ta DCP Abba Kyari da tawagarsa.
Sanarwar da NDLEA ta fitar ta bayyana cewa Afam na da hannu dumu-dumu a harkallar shigo da miyagun kwayoyi na N3bn da ke da alaka da Abba Kyari.
Bayan shafe watanni ana sa ido akansa, an kama Mista Ukatu wanda shi ne shugaban Kamfanin Mallinson Group of Companies, a cikin jirgin da zai je Abuja daga filin jirgin saman Legas, Ikeja a ranar Laraba 13 ga Afrilu.
Hukumar ta ce Afam babban mai shigo da miyagun haramtattun kayayyaki ne, wadanda suka hada da kwayoyin Tramadol da dai sauransu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar hukumar ta NDLEA, wanda ake zargin yana tafiyar da kamfanonin harhada magunguna da yake amfani da su wajen fakewa da shigo da kwayoyin ba bisa ka’ida ba cikin Najeriya, baya ga cewa ya mallaki asusun banki kusan 103 da aka fi amfani da su wajen badakalar kudade.
Hukumar ta tabbar da batun kamun ne ta hanyar wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 25 ga Afrilu.
Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m
Abuja: NDLEA ta kama hodar iblis da aka yi mata basaja a jakunkunan ganyen shayi
A wani labarin, hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana yadda tayi ram da wani Pascal Okolo bayan ta kama shi dumu-dumu da hodar iblis.
A wata takarda da kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a shafinsu na Twitter, ya bayyana yadda aka boye hodar iblis mai nauyin 4.1 kg a jakunkunan shayi.
Ya ce, an ga hakan ne yayin bincikar kayansa na jirgin saman da ya iso Najeriya daga Sao Paulo ta Doha a 17 ga watan Afirilu.
Asali: Legit.ng