Abuja: NDLEA ta kama hodar iblis da aka yi mata basaja a jakunkunan ganyen shayi

Abuja: NDLEA ta kama hodar iblis da aka yi mata basaja a jakunkunan ganyen shayi

  • Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi ta kama wani Pascal Okolo, wanda ake zarginsa da dauko hodar iblis mai nauyin 4.1kg, boye a jakunkunan shayi
  • A kalla an kama masu safarar miyagun kwayoyi guda hudu yayin kokarin shigowa ko fitar da miyagun cikin kasa a makon da ya gabata, wadanda ke tsare a hannun hukumar
  • Kamar yadda kakakin hukumar ya bayyana a wata takarda da ya fita ranar Lahadi, Pascal Okolo ya nuna cewa kasuwancin giya yake daga Brazil

Abuja - Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana yadda tayi ram da wani Pascal Okolo bayan ta kama shi dumu-dumu da hodar iblis.

A wata takarda da kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a shafinsu na Twitter, ya bayyana yadda aka boye hodar iblis mai nauyin 4.1 kg a jakunkunan shayi.

Kara karanta wannan

Matar aure ta sha da kyar, saurayinta ya nemi halakata yayi tsafi da ita

Abuja: NDLEA ta kama hodar iblis da aka yi mata basaja a jakunkunan ganyen shayi
Abuja: NDLEA ta kama hodar iblis da aka yi mata basaja a jakunkunan ganyen shayi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce, an ga hakan ne yayin bincikar kayansa na jirgin saman da ya iso Najeriya daga Sao Paulo ta Doha a 17 ga watan Afirilu.

Babafemi ya ce an sake kama wani jirgi dauke da "miyagun kwayoyi masu nauyin 950g boye a takalman mata" a MMIA, tare da kama wadanda ake zargi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An kama a kalla masu safarar miyagun kwayoyi guda hudu yayin kokarin shigowa ko fitar da miyagun kwayoyi cikin kasar a makon da ya gabata, wandanda suke tsare a hannun hukumar," kamar yadda takardar ta nuna.

Takardar ta kara da cewa:

"Daya daga cikinsu shi ne wani Pascal Ekene Okolo, mai shekaru 33, dan asalin Ihe cikin karamar hukumar Ogwu na jihar Enugu, wanda aka kama yayin bincikensa daga Sao Paulo ta Doha a dakin isowar fasinjoji na NAIA a ranar Lahadi 17 ga watan Afirilu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

"An kama Okolo, wanda ya nuna cewa kasuwancin giya yake a Brazil, tare da jakar matafiya dauke da jakunkunan shayi, wadanda aka yi amfani dasu wajen boye hodar iblis mai nauyi 4.1kg."

'Yan sanda sun yi ram da dillalin kwayoyi a Kano dauke da sinki 250 na wiwi masu darajar N1.7m

A wani labari na daban, jami'an tsaron rundunar'yan sandan jihar Kano sun yi ram da mai safarar miyagun kwayoyi, inda suka samu sunkin wiwi 250 masu darajar N1.7 miliyan, The Nation ta ruwaito.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Juma'a, 15 ga watan Afirilu, ya ce wanda ake zargin Agbo Victor, ya bada labarin yadda ya yi safarar miyagun kwayoyi daga jihar Edo zuwa Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng