Da Dumi-Dumi: Matar tsohon gwamnan jihar Anambra ta riga mu gidan gaskiya

Da Dumi-Dumi: Matar tsohon gwamnan jihar Anambra ta riga mu gidan gaskiya

  • Matar tsohon gwamnan Farko a mulkin farar hula a jihar Anambra, Misis Christiana Njideka Ezeife, ta kwanta dama
  • Gwamnan jihar na yanzu, Farfesa Charles Soludo, shi ya tabbatar da haka, ya kuma kai ziyarar ta'aziyya har gida
  • A cewarsa, wannan ba karamin babban rashi ba ne ga tsohon gwamnan, amma a ko wane lokaci kamata ya yi mutum ya kasance cikin godiyar Allah

Anambra - Misis Christiana Njideka Ezeife, matar gwamnan farar hula na farko a jihar Anambra, Dakta Chukwuemeka Ezeife, ta rasu.

Gwamnan jihar mai ci, Farfesa Charles Soludo, shi ne ya bayyana rasuwar tsohuwar mace lamba ɗaya a Anambra a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Gwamnan Anambra, Soludo yayin da yaje ta'aziyya.
Da Dumi-Dumi: Matar tsohon gwamnan jihar Anambra ya riga mu gidan gaskiya Hoto: Charles Soludo/facebook
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce:

"Rashin masoya na zuwa ne tattare da koma baya a tunani, musamman mutumin da ka gudanar da muhimmin tsagin rayuwarka tare da shi."

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutuwar ranta ya daɗe, Misis Christiana Njideka Ezeife, mata ga tsohon gwamnan Farar hula na farko, Dakta Chukwuemeka Ezeife (Okwadike Igbo Ukwu) babban yankan ƙauna ne a zuciya."

Na kai ziyarar ta'aziyya - Soludo

Gwamnan Soludo ya kuma kai ziyarar ta'aziyya har gida domin jajantawa iyalai da yan uwa bisa wannan babban rashi na jigo a cikin su da suka yi.

Ya ce:

"A yau na je ziyarar ta'aziyya domin jajantawa mai girma tsohon gwamna da kuma iyalansa. Yanayin natsuwa da rungumar ƙaddara da na gan shi a ciki ya tuna mun da cewa a ko wane yanayi muka tsinci kanmu mu gode wa Allah."
"Muna roƙon Allah ya cigaba da ba shi hakurin jure wannan babban rashin, haka nan kuma zamu cigaba Addu'a ga marigayya Mama."

A wani labarin kuma ‘Dan Majalisar Tarayya ya rasu kwatsam, ana shirin fara lissafin babban zaɓen 2023 dake tafe

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi Sallar Jana'izar Alaafin Oba Lamidi Adeyemi

A ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu 2022 mu ka samu labarin mutuwar daya daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya da ke Najeriya, Nse Ekpenyong.

Kafin rasuwarsa, Hon. Nse Ekpenyong shi ne mai wakiltar mazabar Oron a majalisar wakilan tarayya a karkashin babbar jam’iyyar hamayya watau PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262