Dayyabu matukin Adaidaita Sahu ya samu N3m bayan nasara kan yan sanda a kotu

Dayyabu matukin Adaidaita Sahu ya samu N3m bayan nasara kan yan sanda a kotu

  • Wani matukin Keke Napep Dayyabu Anwalu, ya kayar da wasu jami'an yan sanda a kotu kuma ya samu N3m
  • A hoton lauyansa, Abba Hikima, ya daura a Facebook, Dayyabu ya nuna cheque dinsa na kudi
  • Yan Najeriya da dama sun jinjinawa lauyansa bisa jajircewarsa wajen tabbatar da an yi adalci

Kano - Wani matukin Keke Napep Dayyabu Anwalu, ya zama miloniya dare guda. Wannan ya biyo bayan nasarar da ya samu a babban kotun tarayya kan hukumar ladabtar da yan sanda.

Kotu ta yanek hukunci cire N3m daga asusun hukumar yan sandan don biyan Dayyabu bisa cin zarafinsa da yan sanda sukayi.

Dayyabu
Dayyabu matukin Adaidaita Sahu ya zama samu N3m bayan kada yan sanda a kotu Hoto: Abba Hikima
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauya, Abba Hikima, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

A cewarsa:

"Bayan cin tarar hukumar dauka da ladabtar da yan sanda (Police Service Commission )da babbar kotun tarayya (Federal High Court)tayi, Dayyabu ya karbi cekin kudi na Naira Miliyan 3 wanda kotu tace a cira daga asusun bankin hukumar a bashi diyya sakamakon cin zarafin sa da aka yi.
Yan sandan da aka kama da laifi sun hada da Abdullahi Daura, Khalifa da kuma tsohon DPOn Kuntau Police Station Kano wato CSP Abdulhadi."

Abba Hikima ya yi kira da sauran jami'an yan sanda sun daina cin zarafin mutane marasa karfi.

"Da fatan wannan zai zama jan kunne ga yan sanda masu cin zarafin al’umma da ma ita kanta hukumar dauka da ladabtar da yan sanda din," a cewarsa.

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan lamari:

Aliyu Muhammad Tambaya yace:

"Aida ana haka dasun dinga shakka cin zarafin al'umma."

Amir M. Aboki yace:

"Kaaaiii jama'a! Wannan tatsuniya ne ai kudi ba sa hita daga gun Dan Sanda sai dai su shiga"

Kara karanta wannan

Bidiyon Yan Boko Haram 72 sun mika wuya ga Sojoji a Arewa maso gabas

Meenerh Farouq tace:

"Alhamdullah Masha Allah, Allah ya kiyaye gaba ay ko dan dukan da suka lakada masa yaci wadannan kudade."

Asali: Legit.ng

Online view pixel