Dausayin Ramadana: Alamomin da ake gane Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa

Dausayin Ramadana: Alamomin da ake gane Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa

Alamomin da ake gane Daren Laylatul Qadr

Wasu alamomin ana gane su kafin daran, wasu a cikin daran, wasu bayan daran ya wuce.

Shi daren lailatil ƙadri yana da wasu alamomi da ake gane shi da su:

1. Sararin samaniyar wannan daren zai kasance shiru fayau-fayau babu wata hargowa, cikin nutsuwa, babu wata iska mai bugawa da ƙarfi gari ya yi tsit. Kamar yadda Abdullahi ɗan Abbas yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce,

“Shi daren lailatul ƙadri dare ne mai sauƙi, kuma sakakke ba shi da nauyi a jikin mutane da ruhinsu, kuma shi dare ne wanda ba shi da tsananin zafi, ba shi da tsananin sanyi, wato dare ne madaidaici ga jikin ɗan’adam da kuma ruhinsa, don haka rana za ta wayi gari mai rauni marar kaifi kuma ja.”

Kara karanta wannan

Dausayin Ramadana: Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa

2. Samun nutsuwa da kwanciyar hankali a jikin muminai da kuma ruhinsu, saboda saukar Mala'iku a cikin daren, sai Musulmi su riƙa jin wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a zuciyarsu da kuma jikunnansu, ƙirjinsu ya saki ya washe babu nauyi a cikinsa, su sami ɗanɗano da nishaɗi a wajen ibada a cikin daren za su riƙa jin hakan ninkin yadda suka saba ji a wani daren wanda ba shi ba.

3. Mutum zai iya ganinsa a cikin baccinsa, wato a mafarki kamar yadda hakan ya tabbata daga sashin sahabban Ma’aiki ﷺ da waninsu.

4. Idan daren ya gabata washegarin safiyar daren za a ga ranar ta ɓullo wankakkiya fara tas, babu wani gurɓata a cikin ƙwallon haskenta. Kamar yadda hadisi ya zo daga Ubayyu Bn Ka’abu inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce,

Kara karanta wannan

Innalillahi: Farfesan wata Jami'ar Najeriya ya mutu awanni bayan kubuta daga hannun yan bindiga

“Washe garin daren lailatul ƙadri rana za ta bayyana ne ta ɓullo babu gurɓata a cikin haskenta.”

Akwai wasu alamomi kuma na daban waɗanda mutane suke ambaton su waɗanda a gaskiya ba su tabbata daga Ma’aiki ﷺ ba, sai dai ko wataƙila wasu sun gansu ne, kamar a ce, idan daren ya bayyana za a ga bishiyoyi sun kwanta gine-gine sun ranƙwafa, kuma ba za a ji haushin kare ko na jaki a daren ba, da dai sauran su.

A gaskiya dai waɗannan alamomi basu tabbatata da nassin hadisi ko a fatawoyi ingattun malamai ba.

ADDU'AR DA AKE YI A DAREN LAILATUL ƘADRI

An so a yawaita addu'a a goman ƙarshe na watan Ramadhan, musamman ma a dararen da ake tsammanin wucewar wannan dare na lailatul ƙadri, wato su ne dararen (21-23-25-27-29) ana so mutum ya ƙara tsanantawa a wajen nacin addu'a a dare da rana, da fatan samun karɓuwarta, don neman falalarSa, tausayinSa, rahamarSa da kuma karamcinSa a kan bayinSa.

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

Sannan an so ya dage wajen maimaita irin addu'ar da aka jiyo ta daga bakin Ma’aiki ﷺ, kamar yadda Ummina A’ishah take cewa, na ce da Ma’aiki ﷺ ya Ma’aikin Allah ﷺ idan Allah ﷻ Yasa na dace da daren lailatul ƙadri mai kake ganin zan roƙa? Ma’ana wacce addu'a ya kamata in yi? Sai ya ce mata ki ce, “Ya Allah ﷻ kai mai afuwa ne kuma kana son yin afuwa ka yi min afuwa.”

اللهمَّ إنك عفوٌّ تُحبُّ العفوَ فاعفُ عنِّي

Wannan addu'a duk da gajeriya ce a lafazi amma ta shafi duk alkhairin duniya da lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel