Dausayin Ramadana: Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa

Dausayin Ramadana: Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

Malam Daurawa yanzu haka yana gudanar da Tafsirin Ramadanar bana a jihar Gombe.

DAREN LAILATUL ƘADRI

Allah ﷺ ya fifita wani dare a cikin watan Ramadhan ya ba shi wata daraja da ɗaukaka ta musamman, kuma ya keɓance shi da wata falala ta musamman wadda bai bawa sauran darare ba, wannan kuma zaɓi ne da ganin dama ne daga gare shi maɗaukakin sarki, domin yana yin abin da ya ga dama a cikin halittarsa.

Wannan dare shi ne daren lailatul ƙaɗri wanda Allah ﷻ a cikin suratul ƙaɗri ya ce

Ma’ana: “Lallai tabbas cewa mu muka saukar dashi wannan Al-ƙur'anin a cikin dare mai Al-ƙaɗari da matsayi a wajen Allah ﷻ

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Jam'iyyar APC ta faɗi gaskiyar abinda ya sa ta sanya kuɗin Fom Miliyan N100m

Waya sanar da kai menene lailatil ƙaɗari?
Wannan dare mai Al-ƙaɗari ya fi watanni dubu,
Mala'iku suna sauka a cikinsa tare da ruhu (Mala'ika Jibrilu) suna sauka a cikinsa da dukkanin al'amurra, da izinin Ubangijinsu ﷻ,
Waɗannan Mala'iku kalmar aminci kawai suke ta faɗa har zuwa hudowar alfijir.”

Dausayin Ramadana: Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa
Dausayin Ramadana: Daren Laylatul Qadr, Sheikh Aminu Daurawa
Asali: Facebook

Lallai ko ba a faɗa ba, wannan sura ta fito da darajar wannan dare mai albarka, ta fuskoki guda shida, kamar yadda ya zo a cikin AtTafsil litawilit tanzil Malam Musal Adawi ya ce,

❖ Allah ﷻ ya saukar da wannan Al-ƙur’ani a wannan dare kamar yadda ya faɗa a cikin Al-ƙur’ani inda yake cewa: (136) Ma’ana: “Lallai haƙiƙa mu muka saukar da shi a cikin dare mai albarka, haƙiƙa mu masu gargaɗi ne da yin azaba ga kangararru.”

Kara karanta wannan

Matawalle ya rantse da Alkur'ani, ya fallasa wasu manyan mutane dake taimaka wa yan bindiga a Zamfara

❖ Allah ﷻ ya girmama sha'anin wannan dare da ya ce, waya sanar da kai mene ne lailatul-kaɗri?

❖ Yin ibada a cikin daren ya fi yin ibada a wata dubu (1000), wato shekara (83) da wata (2) kenan.

❖ Mala'iku suna sauka acikin wannan daren, kuma an ce, suna sauka ne da rahama, albarka, da kuma nutsuwa, kuma an ce suna sauka ne da dukkan wani al'amari da Allah ﷻ ya zartar, kuma ya ƙaddara shi a cikin wannan shekarar. Aminci da sallama suna sauka a cikin wannan dare ga masu imani da kuma sallamar da Mala'iku suke yi musu.

Abu Hurairah ya ce, Manzon Allah ya ce duk wanda ya tsaya ya yi ibada a wannan dare, da imani da neman lada, Allah ta'ala zai gafarta mana abin da ya wuce na zunubinsa.” ﷺ ya ce,

“Wanda ya yi azumin wannan wata yana mai imani yana kuma neman lada, to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunuban sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel