Kwakwaf: Hotunan da ba kasafai ake gani ba sun nuna abincin da Buhari ke ci a lokacin buda baki

Kwakwaf: Hotunan da ba kasafai ake gani ba sun nuna abincin da Buhari ke ci a lokacin buda baki

  • A karon farko dai 'yan Najeriya za su ga kalar abincin da shugaban kasa Muhammadu ke ci lokacin buda baki
  • Wadannan hotuna dai ba kasafai ake samun irinsu ba, amma wani hadimin Buhari ya yada su a kafar Facebook
  • An samo hotunan ne lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya liyafar buda baki da wasu jiga-jigan gwamnatin Najeriya

Fadar shugaban kasa, Abuja - Watakila saboda wasu dalilai da suka shafi sirri, 'yan Najeriya ba sa sanin wasu lamurran shugaban kasa Muhammadu Buhari, daya daga cikinsu kuwa shi ne yadda da kuma irin abincin da ya fi so, musamman lokacin buda baki.

Amma dai an yi sa'a a wannan karon, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau, ya yada wasu hotunan abin da shugaban kasar ya ci na buda baki a daren Laraba, 20 ga watan Afrilu, tare da wasu jiga-jigan gwamnati.

Kara karanta wannan

Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

Yadda shugaba Buhari ya yi buda baki
Kwakwaf: Hotunan da ba kasafai ake gani ba sun nuna abincin da Buhari ke ci a lokacin buda baki | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari Sallau ya yada wadannan hotunan na shugaban sa ne yayin da ya karbi bakuncin manyan 'yan majalisar dokokin kasar nan domin yin buda baki a fadar shugaban kasa ranar Laraba.

Kamar yadda aka gani a cikin hotunan da aka yadan a Facebook, abincin ba komai bane face ayaba, tuffa, nau'ikan inabi, kosai, da kuma ruwan gora.

Su wa suka haralci taron buda bakin?

Daga cikin wadanda suka halarci liyafar cin abincin akwai shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da mataimakin shugaban majalisar dattawa Ovie Omo-Agege.

Haka kuma, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari da Femi Adesina, daya daga cikin masu taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, duk sun hallara a jiya Laraba.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu

Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

A wani labarin, uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta gayyaci dukkanin yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun siyasa zuwa taron buda bakin Ramadana a fadar shugaban kasa.

Za a gudanar da taron shan ruwan ne a dakin taro na gidan gwamnati a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, da misalin karfe 06:30 na yamma.

A wasikar gayyatan, an umurci yan takarar da kada su zo da wayarsu sai katin gayyatar kawai wanda shine zai basu damar shiga fadar shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel