Yanzu-Yanzu: Ofishin Babban Bankin Najeriya, CBN, Ta Kama Da Wuta
- Gobara ta tashi a wani bangare na ginin Babban Bankin Najeriya, reshen Makurdi da ke Jihar Benue
- Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta taso ne daga wurin ajiyar man fetur na bankin sannan ta yi yunkurin bazuwa
- CBN ta tabbatar da afkuwar gobarar cikin wata sanarwa da ta fitar tana mai cewa ba a rasa rai ba kuma an fara bincike kan sabibin gobarar
Makurdi, Benue - Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa ana gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Makurdi, Jihar Benue a ranar Alhamis, 21 ga Afrilun, 2022, rahoton The Nation.
Daily Trust ta tattaro cewa gobarar ta tashi ne misalin karfe 7 na safiyar yau amma jami'an hukumar Kwana-kwana sun kawo dauki sun dakile wutar kafin ta bazu.
Ginin na CBN da ke Makurdi yana kusa da gidan gwamnatin jihar ne kuma yana kallon bankin United Bank of Africa, UBA, reshen Makurdi.
Wasu shaidan gani da ido sun magantu kan yadda gobarar ta afku
Wasu ganau sun tabbatar da afkuwar lamarin inda suka ce sun gano wuta daga bayan ginin bankin da ke tsohuwar GRA a Makurdi.
"Misalin karfe 7 na safiyar yau ne muka lura wuta na ci bal-bal a ginin bankin," in ji Stanley.
An kuma gano cewa gobarar ta tashi ne daga wurin ajiyar man fetur na bankin amma nan take wutar ya bunkasa hakan yasa wasu ma'aikatan suka lura suka janyo hankalin mahukunta.
Hukumar Kwana-Kwana na Jihar Benue Ta Kai Dauki
Da aka tuntube shi, Direktan Hukumar Kwana-Kwana na Jihar Benue, Donald Ikyaaza, ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma ya ce an kira su kuma ya tura mutanensa nan take.
Ikyaaza ya ce:
"Babban wuta ne sosai wadda ta tashi daga wurin ajiyar fetur na kamfanin, amma mutane na sun garzaya wurin sun kashe wutan kafin ya bazu zuwa wasu wuraren. Yanzu hankula sun kwanta."
A lokacin da wakilin The Punch ya isa wurin misalin karfe 10.45 na safe, jami'an tsaro sun zagaye wurin. Sun kuma kori mutane daga wurin.
Babban Bankin Najeriya, CBN, ta magantu kan gobarar
Sanarwar da CBN ta fitar a shafinta na Twitter ya tabbatar da afkuwar gobarar. Sanarwar ta ce wutan ya tashi ne daga wurin ajiyar man fatur da ke bayan ginin bankin misalin karfe 7 na safe.
Sai dai hukumar kwana-kwana ta Jihar Benue ta amsa kira ta kuma kashe wutar a halin yanzu ana bincike yayin da an cigaba da ayyuka kamar yadda aka saba.
Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.
An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.
Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.
Asali: Legit.ng