Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja
- An samu labarin mutuwar wata mata da aka fi sani da Mama Tobi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja
- Ganau sun tabbatar da cewa, matar za ta iya rayuwa, idan da a ce tawagar likitocin FAAN na wurin da lamarin ya auku
- Duk iya kokarin da aka yi wajen ganin an garzaya da ita asibitin filin jirgin, bai yi tasiri ba saboda babu likitocin da zasu duba marigayiyar
Abuja - Wata fasinjar jirgin sama, wacce aka fi sa ni da Mama Tobi ta yanke jiki ta fadi inda ta mutu a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, The Nation ta ruwaito.
Kamar yadda jaridar ta bayyana, wani lauya mai suna Che Oyinatumba ne ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ganau din ya wallafa bidiyoyin a shafinsa na Facebook, inda ya nuna yadda lamarin ya auku.
Kamar yadda bidiyon ke nunawa, an ga wasu fasinjoji na yi wa matar da ba a san ko wacece ba addu'o'i bayan ta yanke jiki ta fadi.
Oyinatumba ya ce:
"Tsawon mintina 13, babu wani daga cikin tawagar likitocin FAAN. A hannuna da wasu ta mutu. Wani likita dake kan hanyarsa na zuwa Kano ya yi kokarin ceto ranta, amma daga karshe ya ce 'Mun rasata'. Da a ce FAAN ta samar da allurar insulin da bata rasa ranta ba."
Kamar yadda wallafar ta nuna, an gano yadda matar ke da ciwon suga, yayin da wasu daga cikin fasinjoji suka yi kokarin kawo mata agaji daga likitocin hukumar jirgin saman tarayyan Najeriya, ba tare da samun wadanda zasu ceto ranta ba.
Yadda FAAN ta nuna halin ko in kula
Ganau din ya kara da bayyana yadda jami'an FAAN da na jirgin saman suka nuna halin ko in kula, yayin da aka fara neman agaji.
A cewarsa: "Ba muyi kasa a guiwa wajen kiran sunanta ba, Mama Tobi, Mama Tobi, kada ki tafi ki bar mu, ki tashi, da sanyin safiyar nan, amma yawunta ya dalalo kasa, inda bakinta ya fara kumfa, daga nan ne muka fahimci cewa ruhinta ya yi kaura daga jikinta, kuma ba za ta dawo ba!
"FAAN da sauran ma'aikatan jirgin saman dake wurin sun nuna halin ko in kula kamar hakan bai shafesu ba.
"Sun cigaba da shelar daukar fasinjoji, ba tare da tambayar ko akwai wani likita a wurin ba."
Haka zalika, ganau din ya cigaba da labarta yadda wasu fasinjoji suka je neman agaji a karamin asibitin, sai dai yayin da suka isa wurin, babu wanda zai duba su.
An bayyana yadda fasinjoji suka yi kokarin ganin sun nemi agajin motar daukar gawa daga sashin kula da gobara a filin jirgin don ta zo ta dauke gawar.
Daga bisani, wata majiya, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce, ba zai iya tabbatar da mutuwar matar ba, amma yana da tabbacin yadda matar ta fita daga hayyacinta a lokacin da lamarin ya auku.
Asali: Legit.ng