Jerin Haɗurran Jiragen Sojojin Najeriya da Suka Faru a Cikin Shekarar 2021

Jerin Haɗurran Jiragen Sojojin Najeriya da Suka Faru a Cikin Shekarar 2021

Wannan shekarar 2021 da ta gabata ta kasance mai cike da ƙalubale a Najeriya saboda samun haɗurran jiragen sama wanda ya laƙume rayuka da yawa

Tun daga haɗarin farko a Abuja har zuwa wanda ya faru na ƙarshe a Zamfara, rundunar sojin Najeriya ta samu kaƙubalen hatsarin jiragenta hudu a 2021.

Jirgin rundunar sojojin sama NAF.
Jerin Haɗurran Jiragen Sojojin Najeriya da Suka Faru a Cikin Shekarar 2021
Asali: Getty Images

1. Haɗarin jirgin sojoji a kusa da Abuja

A ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairu, 2021, jirgin rundunar sojin sama (NAF) King Air 350 ya yi hatsari a kusa da Abuja, inda lamarin ya lakume rayukan baki ɗaya jami'ai Bakwai dake ciki.

A bayanan Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, jirgin ya yi haɗari ne jim kaɗan bayan tura saƙon cewa injinsa ya samu matsala.

Kara karanta wannan

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna

2. Jirgin NAF 474 ya kauce wa hanya

Ranar Laraba 31 ga watan Maris, 2021, Jirgin sama NAF474 mallakin rundunar sojin sama ta Najeriya ya kauce wa hanyar da ake kula da shi.

Jirgin wanda ke ɗauke da sojoji biyu yana kan hanya ne zuwa Borno domin taimaka wa Dakaru yaƙi da mayaƙan Boko Haram. Duka mutum biyun suka rasu.

3. Haɗarin jirgi a Kaduna

A wata ranar Jumu'a 21 ga watan Mayu, 2021, Jirgin Sojoji ya yi hatsari a Kaduna, ya kashe shugaban rundunar sojin ƙasa, Ibrahim Attahiru, da wasu jami'an soji 10.

Manyan jami'an sojojin suna kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja lokacin da mummunan lamarin ya rutsa da su.

4. Hatsarin Jirgin Sojoji a Zamfara

Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) a ranar 19 ga watan Yuli, 2021 ta tabbatar da faɗuwar jirginta a kan hanyarsa ta dawowa daga wani aiki wanda aka ci nasara.

Kara karanta wannan

Jirgin Super Tucano ya yi wa ISIS lahani, ya kashe ‘Dan ta’addan da ake takama da shi

Kakakin NAF, Edward Gabkwet, shi ya bayyana haka a wata sanarwa a ya fitar kuma aka aike wa jaridar Legit.ng Hausa.

Bisa nasara, matukin jirgin ya samu nasarar tsira da rayuwarsa bayan ya zare kan shi daga cikin jirgin, wanda yan ta'adda suka kakkaɓo.

A 2021 kaɗai Sojojin Najeriya sun rasa jami'ai 20 sanadiyyar haɗarin jirgin sama cikin su har da tsohon hafsan rundunar sojojin ƙasa.

A wnai labarin kuma Bayan gana wa da Buhari, gwamnan Imo ya fallasa wasu yan siyasa dake ɗaukar nauyin yan bindiga a Najeriya

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce yanzun ba shi da wata tantama kan mutanen dake ɗaukar nauyin 'yan bindiga.

Bayan gana wa da shugaba Buhari a Aso Villa, Uzodinma ya roki yan siyasa su daina siyasa da gaba, su yi siyasa da tsafta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel