Gwamna Zulum ya yi rabon buhuhunan hatsi da kudi ga mutum 100,000 a cikin garin Maiduguri da Jere
- Kamar yadda ya saba, gwamnan Borno da kansa ya fara rabon kayan hatsi da al'ummar jiharsa cikin azumi
- Yan kwanaki bayan ziyarar da ya kai Monguno rabon abinci irin wannan, Zulum ya dire Jere wannan karon
- Mutane a kafafen labarai da sada zumunta sun zubawa gwamnan na Borno albarka
Maiduguri - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da rabon kayan abinci ga mutum 100,000 mazauna cikin garin Maiduguri da karamar hukumar Jere.
Zulum ya kaddamar shirin rabon a farfajiyar wakshon kanikanci dake Maidguri ranar Talata.
Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar da yammacin Talata a shafinsa na Facebook.
Zulum ya raba buhuhunan abinci, kudi, da turmin atamfa ga iyalai.
Yace an yi wannan rabon ne domin rage radadin halin da manoma ke ciki sakamakon rashin iya zuwa gonakinsu noma.
Yace:
"Da yawa daga cikn matasanmu da marasa galihu sun gaza zuwa gonakinsu kuma hakan ya sa gwamnatin jihar Borno ta yanke shawarar cigaba da baiwa mabukata abinci a jihar."
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Kakakin majalisar dokokin jihar, Shugaban masu rinjaye a majalisar jihar, kwamishanoni, dss.
Kalli hotunan:
Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yayin da ya kai ziyara babban asibitin a Konguno, ranar Asabar, ya sanar da amincewa da karin kashi 30 cikin dari na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai ba tare da tsammani ba.
Baya ga likitoci, ma'aikatan lafiya, anguwan zoma, masu gwaje-gwaje a dakin bincike, masu hada magunguna da sauran ma'aikatan lafiya na kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin kashi 30 bisa dari na albashinsu, don karfafasu wajen gudanar da aiki mai nagarta da kula da fannin lafiya yadda ya dace.
Kananan hukumomin: Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da Banki cikin Bama wanda suke daga cikin wuraren da 'yan Boko Haram suka tarwatsa a shekarar 2014, ba tare da an zauna ba na kusan shekaru takwas har zuwa rufe sansanin 'yan gudun hijara da masu neman mafaka aka yi.
Asali: Legit.ng