Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

  • Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ce gwamnati ba za ta rintse idanu akan hatsarin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’adda ba
  • Ya fadi hakan ne yayin da ya ke amsar tubabbun ‘yan ta’addan, inda ya ce akwai bukatar samar da tsaro mai yawa da kuma bin hanyoyin kare kowa a jihar
  • Gwamnan ya ce addu’o’in mutanen da ke fadin duniya ne suka kawo tarin nasarorin da har ta kai ga fiye da mayakan ISWAP da Boko Haram 35,000 suka zubar da makamansu

Borno - Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno yayin da yake amsar tubabbun ‘yan ta’adda ya ce gwamnati ba za ta makance wa hadarorin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’addan ba, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, akwai bukatar tsananta tsaro da kuma bin hanyoyi da dama wadanda zasu cire hadarorin da ke tare da shirin, kuma su tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Sauya Tunanin Tubabun 'Yan Ta'adda
Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Sauya Tunanin Tubabun 'Yan Ta'adda, In Ji Gwamna Zulum. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya kwatanta tubar mayakan Boko Haram da ISWAP fiye da 35,000 a matsayin taimako daga Ubangiji sakamakon addu’o’in mutane daban-daban na duniya.

The World News ta nuna yadda yayin bikin Easter, Zulum ya ce zubar da makaman da mayaka fiye da 35,000 suka yi wata mu’ujiza ce ta Ubangiji don kawo zaman lafiya a Jihar Borno da sauran yankuna a Arewa maso Gabas.

Ya yi barar addu’a daga mutane don samun nasara akan shirin

Kamar yadda ya ce:

“Zub da makaman da ‘yan ta’adda da dama suka yi alama ce da ke nuna Ubangiji ya amshi addu’o’in mutanen Jihar Borno, yankin Arewa maso Gabas, Najeriya da kuma duniya baki daya, masu yin addu’ar Ubangiji ya kawo karshen ta’addanci a Jihar Borno.
“Wajibi ne mu dage wurin gyara da kuma raba tubabbun ‘yan ta’addan da makamai. Sannan wajibi ne mu amshe su ba tare da kallon hadarin da ke tattare da shirin sabunta musu dabi’u ba. Sannan mu tabbatar mun tsare kowa da kowa.

Kara karanta wannan

2023: Abu ɗaya zai kawo karshen yan bindiga a Najeriya, Gwamnan dake son gaje Buhari ya gano

“Ina barar addu’ar gaba daya ‘yan Jihar Borno akan samun nasara dangane da shirin nan, da kuma nasarar jami’an tsaro da ‘Yan Sa Kai wadanda ke taimakawa wurin dakile ta’addanci.”

Ya kara da cewa fiye da shekaru 12 ana yaki da ta’addanci a Jihar Borno, a karon farko Ubangiji ya kawo mafitar kawo karshen ta’addanci.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164