Halin bera: Yadda sabon ma'aikaci ya tsere da cinikin rana guda na gidan burodi

Halin bera: Yadda sabon ma'aikaci ya tsere da cinikin rana guda na gidan burodi

  • Wani sabon ma’aikaci a gidan burodin Tasty Loaf Bakery ya tsere da makudan kudin kamfanin bayan daukarsa aiki
  • A cewar masu gidan burodin, wanda ake zargi da aikata laifin ya fara aikin ne ba da jimawa ba, wanda yasa aka yarda dashi
  • Sai dai tun farko an gargade su da kada su dauke shi aiki saboda laifukan da ya aikata a baya amma suka yi kunnen uwar shegu

Jihar Legas - Wani sabon ma’aikacin gidan burodi mai suna John Emeka ya tsere da kudi naira 350,000 na kamfanin da yake aiki da shi.

Emeka wanda rahotanni suka ce ya samu aiki a gidan burodin Tasty Loaf a kan titin Ajelogo, Mile 12, jihar Legas, an gan shi ta kyamarar CCTV na kamfanin yana tserewa da kudaden, wanda aka ce jimillar ciniki ne na ranar Laraba, 16 ga Maris.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

Yadda wani ya fece da kudaden cinikin wani kamfanin burodi
Mai hannun bera: Sabon ma'aikacin gidan burodi ya fece da kudi N350,00 ranar da aka dauke shi aiki | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kamfanin ya kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Mile 12 a jihar ta Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa, ya bar wayarsa da ba ta dauke da layin SIM ya tsere zuwa Ibadan a jihar Oyo, kamar yadda binciken bin diddigin layinsa ya nuna.

Da take tofa albarkacin bakinta kan lamarin, mai kamfanin, Motunrayo Odusi, ta ce kamar yadda kyamarar CCTV ta nuna, wanda ake zargin ya tsere da kudaden ne da misalin karfe 5:48 na yamma, Punch ta ruwaito.

Ta ce:

“Mijina ne ya hadu da Emeka a wani gidan cin abinci inda yake aiki, daga baya ya gabatar da abokinsa, Victor ga mijina kuma ya roki mu dauke shi aiki.
“Ya kira mijina ta waya bayan wata daya da ya rasa aikinsa a gidan cin abinci ya roki a ba shi aiki, sai muka amince muka dauke shi aiki a gidan burodinmu.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

“Kusan makonni biyu bayan daukarsa aiki Emeka ya tambaye shi ko zai iya zama a masaukin gidan burodin saboda yana da matsalar masauki nan ma muka amince."

Ta kuma bayyana cewa, Emeka ya samu alaka ta kai tsaye da kudin kamfanin ne tun bayan da ma'aikacin lura da kudin kamfanin ya ajiye aiki.

Da take karin haske, ta ce da ma abokin mijin nata; Victor ya gargadesu da kada su dauki Emeka aiki kasancewarsa ya taba tafka wata aika-aikar.

A nasa bangaren, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundenyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa, babu wata takarda da ke nuna wanda ya tsayawa Emeka har aka dauke shi a gidan burodin.

An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

A wani labarin, kwanaki biyar kenan da majalisar kolin Najeriya ta yi afuwa ga wasu mutane 159 da aka samu da laifi, amma har yanzu ba su samu ‘yanci ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Wani rahoto da ya fito daga Punch a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu 2022 ya bayyana cewa Joshua Dariye da Jolly Nyame su na tsare har yanzu.

Tsofaffin gwamnonin na jihohin Taraba da Filato ba za su fito daga gidan gyaran hali ba, har sai Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya sa hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.