Yanzu-Yanzu: Mayaƙan ISWAP Suna Can Sun Kai Wa Sojoji Hari A Sansaninsu Da Ke Borno
- 'Yan ta'ddan kungiyar ISWAP suna can sun afka wa sojojin Najeriya hari a sansaninsu da ke Molai a ƙaramar hukumar Jere a Borno
- Rahotanni sun ce mutanen gari sun tarwatse suna ta tserewa yayin da aka ce an hangi karin dakarun sojoji suna hanyarsu ta zuwa garin
- Majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da harin tana mai cewa dakarun tsaro suna daukan matakan dakile hari a halin yanzu
Jihar Borno - Mayaƙan kungiyar ta'addanci ta Islamic State in West Africa Province (ISWAP) suna can sun kai hari sansanin sojoji a Borno.
Daily Trust ta tattaro cewa ƴan ta'addan sun kai hari sansanin sojoji ne da ke Molai a ƙaramar hukumar Jere a daren ranar Litinin.
A cewar majiya ta tsaro, mazauna garin sun tsere sun nufi ofishin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, FRSC, a yayin da ake musayar wutan, rahoton Daily Trust.
"A halin yanzu da muke magana, mayakan ISWAP sun kai hari sansanin sojoji, mutanen suna tserewa kuma an ga sojoji suna bin hanyar Molai. Muna daukan mataki kan abin," in ji majiyar.
'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed
A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.
Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.
Asali: Legit.ng